Gwamnonin APC 20 sun bukaci kafa kwamitin tsara gangamin jam'iyyar
Mun samu rahoton cewa, gwamnoni 20 cikin 24 na jam'iyyar APC sun rattaba hannu kan wata wasika domin isarwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana bukatar su wajen kafa sabon kwamitin da zai tsara gangamin jam'iyyar.
Gwamnonin sun yi wannan hobbosa domin neman shugaba Buhari ya amince da kafa sabon kwamitin da zai tsara taron jam'iyyar da za a gudanar a watan Yuni wajen zaben sabbin shugabannin jam'iyya.
Da sanadin binciken diddigi daga karfafan majiyoyi, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tun a ranar da ta gabata ne wasu daga cikin gwamnonin suka fara rattaba hannu kan wannan wasika daya bayan daya, sakamakon jayayya tare da tayar da jijiyoyin wuya da ta afku a yayin ganawar gwamnonin tare da shugaba kasa a fadar sa ta babban birnin tarayya.
Jaridar ta kuma ruwaito cewa, kawowa yanzu gwamnoni 15 sun rattaba hannayen su a wasikar da suka hadar da; Rochas Okorocha na jihar Imo, Abdul-Aziz Yari na jihar Zamfara, Abdullahi Ganduje na jihar Kano, Kashin Shettima na jihar Borno, Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato, Abubakar Bagudu na jihar Kebbi, Akinwunmi Ambode na jihar Legas da kuma Abiola Ajimobi na jihar Oyo.
Sauran gwamnonin da suka rattaba hannu sun hadar da; Abubakar Bello na jihar Neja, Samuel Ortom na jihar Benuwa, Andrew Obaseki na jihar Edo, Ibikunle Amosun na jihar Ogun, Rauf Aregbesola na jihar Osun, Umaru Tanko na jihar Nasarawa, Muhammad Jibrilla na jihar Adamawa, Abdul-Fatah Ahmed na jihar Kwara da kuma Muhammad Badaru na jihar Jigawa.
Majiyar ta kuma ruwaito cewa, akwai gwamnoni uku na jam'iyyar da ba su halarci ganawar ranar Talata ba sakamakon wata tafiya da suka yi zuwa kasashen ketare. Gwamnonin sun hadar da; Aminu Bello Masari na jihar Katsina, Ibrahim Gaidam na jihar Yobe da kuma Muhammad Abubakar na jihar Bauchi.
KARANTA KUMA: Jerin Jihohi 16 da suka sha fama da cutar Sankarau a Najeriya
Jaridar Daily Trust ta fahimci cewa, a yayin da ake sa ran hadin kan gwamnonin jihar Yobe da na Katsina, akwai yiwuwar gwamnan jihar Bauchi ya aikata kishiyar hakan sakamakon kasancewar sa na hannun daman ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.
Sauran gwamnoni hudun da ke goyon bayan tsawaita wa'adin Cif John Odigie-Oyegun, shugaban jam'iyyar a kujerar sa, sun hadar da; Mallam Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna, Simon Bako Lalong na jihar Filato, Rotimi Akereolu na jihar Ondo da kuma Yahaya Bello na jihar Kogi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng