Taskar Kannywood: An yi ma Ali Nuhu kishiya, za’a nada Adam A Zango Sarkin Kannywood

Taskar Kannywood: An yi ma Ali Nuhu kishiya, za’a nada Adam A Zango Sarkin Kannywood

A wani mataki mai daukan hankali a sa-toka sa-satsi dake tsakanin Sarkin Kannywood, Ali Nuhu da yaronsa, Adam A Zango, masu kallon fina finan na Kannywood sun kammala shrin nada A Zangon a matsayin ‘Sarkin Yan Fina Finan Hausa.”

Rariya ta ruwaito shugaban riko na kungiyar masu kallon fina finan Hausa ta kasa, Fala M Shareef yana bayyana dalilinsu na nada Zango wannan muhimmin mukami, inda yace sun hada da hakurinsa, iliminsa, kyautarsa, ibadarsa, mutuncinsa, halin yafiya da biyayyarsa ga na gaba.

KU KARANTA: Masarautar Daura ta tafka babbar asara da mutuwar Sanata Mustapha Bukar –Mai martaba Sarkin Daura

Fala ya cigaba da zayyano ma majiyar Legit.ng dalilansu na nada A Zango Sarkin Fina Finan Hausa,inda yace Zango furodusa ne, Darakta ne, makadi ne, mawaki ne, edita ne, jarumi ne, kuma ya iya taka rawa.

Taskar Kannywood: An yi ma Ali Nuhu kishiya, za’a nada Adam A Zango Sarkin Kannywood
Adam A Zango Sarkin Kannywood

Sai dai yace basu nada A Zango Sarki ba da nufin kuntata ma wani, sai kawai don shi ne yafi cancanta, “Kuma ai dama babu wani Sarki a Kannywood. Asali ma wannan kyauta ba mu muka bada shi ba, daga Allah ne” Inji shi

A yanzu haka tuni masoya da masu fatan alheri ga Zango suka shirya masa wani gagarumin biki a jihar Nassarawa don bayyana masa goyon bayansu tare da taya shi murna, inda suka cika a taron, yawancinsu sanye da kayan sarauta

Daga karshe masoyan A Zango sun tabbatar da cewa akwai sauran hidima a ranar nadin sarautar, kuma ba zasu kara bari wani ko wata duk girmansa, duk kankantansa ya ci zarafin jarumin ba, inda suka ce zasu dauki mataki kan duk wanda ya nemi tozarta gwaninsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel