Kanu Nwankwo ya karyata kishin-kishin din cewa zai fito Shugaban kasa
- Da mun ji Tsohon ‘Dan kwallon kasar nan Kanu zai yi takara
- Nwankwo Kanu yace bai da shirin fitowa zabe a shekarar 2019
- Goal.com wasa ta ke yi lokacin da aka fitar da rahoton a baya
A da an ji cewa Tsohon kyaftin din Super Eagles na ‘Yan kwallon Najeriya Nwankwo Kanu zai yi takarar Shugaban Kasa a zabe mai zuwa 2019 da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Tsohon ‘Dan wasan Arsenal Nwankwo Kanu mai shekara 41 a Duniya ya karyata rade-radin cewa yana da niyyar takarar Shugaban Kasa a zabe mai zuwa. Kanu yace wasa ne kurum Goal.com tayi kamar yadda aka saba a farkon watan Afrilu.
KU KARANTA:
Shi dai tsohon ‘Dan wasan gaban Super Eagles Kanu Nwankwo yace abin da ya dame shi a kasar shi ne ya ga matasan Najeriya sun kware a harkar wasanni. Kanu yana da gidauniyar da ya bude da ta take taimakewa marasa lafiya a kasar.
A shekarar bara ne tsohon Gwarzon Afrika ‘Dan wasan kwalon kafa George Weah ya lashe zaben kasar Liberiya bayan ya fitar da Mataimakin Ellen Johnson Sirleaf. Shi dai Nwankwo Kanu yace ba siyasa ta ke gaban shi ba a halin yanzu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng