Gudun wuce sa'a: Mutum biyu sun mutu a hatsarin tawagar matar gwamna
Hankula sun tashi a jihar bayan da mata biyu suka mutu a hatsarin mota da ya ritsa da tawagar Nkechi Ikpeazu, matar gwamnan jihar Abiya, Ikpeazu.
Promise Uche-Nwamkpa, daya daga cikin matan da suka mutu, mata ce ga wani tsohon dan majalisar jihar, yayin da daya matar, Nwamaka Maduchukwu, mai taimakawa gwamnan jihar, Ikpeazu, ce a kan kafafen watsa labarai.
Hatsarin ya afku ne a hanyar dawowar tawagar daga Ntigha-Uzor dake karamar hukumar Obingwa, inda gwamna Ikpeazu ya halarci bikin binne gawa.
Wani shaidar gani da ido ya ce hatsarin ya afku ne sanadiyar kokarin wuce wata mota da direban dake dauke da matan da suka mutu ya yi, a yayin da yake tsaka da gudun wuce sa'a.
Shaidar ya ce motar ta wuntsila sau uku da mutanen dake ciki.
DUBA WANNAN: Buhari zai yi wani bulaguro na sirri zuwa birnin London sati mai zuwa
Kazalika wata mata da ta tsira ba tare da samun koda kwarzane ba, ta tabbatar da cewar direban motar na gudun wuce sa'a.
A lokuta da dama, 'yan Najeriya kan koka a kan gudun wuce mizani da tawagar masu mulki kan yi a manya da kananan tituna.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng