Dasuki: Wani tsohon Gwamna ya bayyana dalilin da ya sa karbi Miliyan 500 lokacin zabe

Dasuki: Wani tsohon Gwamna ya bayyana dalilin da ya sa karbi Miliyan 500 lokacin zabe

- Jam’iyyar PDP ta wanke tsohon Gwamnan Oyo Rashid Ladoja daga zargi

- Ladoja na cikin wadanda aka fitar da sunan su cikin jerin barayin Najeriya

- PDP ta gargadi Shugaba Buhari cewa yanzu fa ba lokacin mulkin Soja bane

Jiya mu ka samu labari dagaa Premium Times cewa tsohon Gwamnan Jihar Oyo Rasheed Ladoja yayi karin game da kudin da ya karba har Naira Miliyan 500 daga hannun Sambo Dasuki a lokacin yakin neman zabe a 2015.

Dasuki: Wani tsohon Gwamna ya bayyana dalilin da ya sa karbi Miliyan 500 lokacin zabe
Sunan Rashidi Ladoja ya fito cikin barayin Najeriya

Jam’iyyar PDP ba ta ji dadi da ta ji an sa Rashidi Ladoja cikin wadanda su ka saci kudin kasar ba. PDP tace Sanata Ladoja ya karbi kudi ne daga hannun Sambo Dasuki na wani gidan sa da ya saida masa da ke cikin Garin Legas.

KU KARANTA: Ana zargin an samu wasu kudi a gidan Jonathan

PDP tace wani katafen gida ne tsohon Gwamnan ya saidawa Sambo Dasuki a kan Naira Miliyan 600 wanda ya biya Miliyan 500. Sai dai kafin a iya cika ragowar kudin ne Dasuki ya bar ofis inji Jam’iyyar adawan na reshen Oyo.

Don dole ne dai Jam’iyyar ta fito tayi wa jama’a bayanin gaskiyar abin da ya faru. PDP tace ba ta sha’awar sata amma fa duk da haka ta kuma gargadi Shugaba Buhari da ya bi doka wajen yaki da barna don shi ba Soja bane yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng