Fitacciyar jarumar Kannywood, Zee Zee ta watsa hotunan Saurayinta suna soyewa
Tsohuwar tauraruwar fina finan Kannywood, Ummi Ibrahim, da aka fi sani da suna Ummi Zee Zee ta bayyana wasu hotuna irin na soyayya, tare da sabon Saurayinta, Soja, inji rahoton Kannywood Scene.
Majiyar Legit.ng ta daura hotunan Ummi Zee Zee tare da saurayinta ne a shafinta na sadarwar zamani, Facebook, inda aka hangi Zee Zeen tana rungume da saurayin nata, wanda aka bayyana shi a matsayin Soja.
KU KARANTA: Wani babban Limami ya hallaka budurwasa, ya binne gawarta a dakin bautansa
A wani labarin kuma, jaridar Daily Post Hausa ta ruwaito Zee zee na cigaba da sukar gwamnatin APC karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ta gargadi yan Buhari da su fita daga idonta.
Zee Zee tace: “Duk yawanku bana tsoron fuskantarku wajen yi muku RADDI domin ni a rayuwata ban san wani abu da ake kira tsoro ba, balle tsoron wani kato ya taka min birki wajen fadar gaskiya akan ra'ayina dangane da harkar siyasa.
“Ni Allah kadai nake tsoro ba mutum mai rauni iri na ba, kuma kun sanni in na tashi magana akan APC magana daya nakeyi wadda take girgiza kasar gaba daya.” Inji ta.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng