Nigerian news All categories All tags
An kama wata budurwa Kirista yayin da take tafka mummunar ta’asa sanye da Hijabi da Nikabi (Hoto)

An kama wata budurwa Kirista yayin da take tafka mummunar ta’asa sanye da Hijabi da Nikabi (Hoto)

Karshen tika tika tik inji Hausawa, hakazalika karshen alewa kasa kamar yadda ake fada, kwatankwacin haka ne ya faru da wata budurwa da Allah ya tona ma asiri, kamar yadda Rariya ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito dubun wata budurwa Kirista mai suna Grace ya cika bayan ta shirya nufin bata ma addinin Musulunci suna, inda ta sanya Hijabi da Nikabi, ashek zata fita aikin sata ne.

KU KARANTA: An bankado yadda Sambo Dasuki ya taimaka ma Buhari wajen darewa kujerar shugaban kasa a karo na farko

Wannan lamari ya faru ne a garin Kisi na jihar Oyo, inda Grace take satar kayayyakin jama’a tana sanye da Hijabi da nikabi, ta yadda idan aka kamata za’a yi zaton Musulma ce, ba’a san kuwa ba haka bane.

An kama wata budurwa Kirista yayin da take tafka mummunar ta’asa sanye da Hijabi da Nikabi (Hoto)

Budurwar

Dayake Allah ba azzalumin bawansa bane, sai asirinta ya tonu, bayan jama’an garin sun kamata, sa’annan suka yi mata rubdugu, tare da mika ta ga hannun rundunar Yansandan yankin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel