An gano mutumin da ya zamar wa Atiku kadangaren bakin tulu a siyasa

An gano mutumin da ya zamar wa Atiku kadangaren bakin tulu a siyasa

Cif Ufuoma Charles Obule,, masoyin Atiku kuma dan takarar kujerar Sanata a jihar Legas Delta, ya bayyana Obasanjo a matsayin mutumin da ya zamewa Atiku kadangaren bakin tulu a burinsa na son mulkin Najeriya.

Obule ya bayyana hakan ne yayin taron bude wani ofishin yakin neman zaben Atiku a matsayin shugaban kasa a zaben 2019 da ka yi a Effurun dake karamar hukumar Uvwie a jihar Delta.

Obule, bako na musamman a wurin taron, ya ce a ba zasu bari Obasanjo ya basu matsala ba a wannan karon.

An gano mutumin da ya zamar wa Atiku kadangaren bakin tulu a siyasa
Atiku Abubakar

"Zamu dakatar da shi wannan karon. Dole Obasanjo ya fita sabgar mu, ba zamu yarda ya cigaba da dasa mana mutane a matsayin shugaban kasa ba," inji Obule.

Kazalika, Obule, ya bukaci matasan Najeriya da su tashi tsaye su hada kansu wuri guda domin yaki da mulkin mulaka'u da wasu mutane ke yi a kasar nan.

DUBA WANNAN: Ganawar Buhari da gwamnonin APC: Hotuna da rahoton abinda ya faru

A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar, an kone wani matashi dake sansanin 'yan gudun hijira dake garin Ikang a jihar Kuros Riba, ranar Asabar, bisa zarginsa da satar N4,000.

Rahotanni sun bayyana cewar matashin mai shekaru 26 ya bar sansanin 'yan gudun hijirar, mai nisan kilomita 25 daga birnin Kalaba, domin sayen wasu kayayyaki amma sai ya saci kudi a shagon da ya je siyayyar, hakan ya saka wasu matasa yi masa wannan danyen hukunci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng