Jerin kasashe 10 da sukafi yawan al'umma a nahiyar Afirka
Shin ko ka san kasar da tafi yawan al'umma a nahiyar Afirka? Akwai kasashe masu yawa a nahiyar ta Afirka kuma akwai miliyoyin al'umma masu harsuna, addinai da kabilun daban-daban da ke zaune a cikin su. Don sanin kasashen da sukafi yawan al'umma, bari mu duba alkalluman kididiga.
Ko ka san cewa kasar ka ta Najeriya itace tafi kowanne kasa a Afirka yawan al'umma?
1) Najeriya.
Najeriya ce kasar da ke kan gaba wajen yawan al'umma a nahiyar Afirka. Alkalluman kididiga a halin yanzu suna nuna cewa mutanen da ke Najeriya sun kai billiyan 194,556,463 kamar yadda kididigar da Majalisar Dinkin ta fitar a watan Maris din 2018 ya nuna.
A duniya, Najeriya ce kasa ta bakwai wajen yawan al'umma. Adadin al'ummar da ke Najeriya sun kai 2.5% na mutanen duniya. Najeriya tana da fadin kasa wanda ya kai 910,770km2 kuma galibin mutanen Najeriya na zama a birane ne.
2) Ethiopia
Bayan Najeriya, kasar Ethiopia ce ta biye da ita wajen yawan al'umma a Afirka. A halin yanzu adadin mutanen da da zaune a kasar Ethiopia sun kai miliyan 107,534,882 kuma alkalluman kididiga sun nuna cewa yawan al'ummar kasar na karuwa sosai.
3) Egypt
Kasar Misra ne take biye da kasar Ethiopia wajen yawan al'umma a Afirka, daga shekarar 1955 adadin al'ummar da ke Egypt ya karu daga miliyan 25,523,384 zuwa miliyan 99,375,741 a halin yanzu kamar yadda alkalumma suka nuna.
KU KARANTA: Komai nisan jifa: An kama dukkan 'yan dabar Dino Melaye da suka tsere daga hannun 'yan sanda, ku kalli fuskokinsu
4) DR Congo
Jamhuriyyar Demokradiyar Congo itace kasa na hudu wajen yawan al'umma a Afirka, kasar na da adadin al'umma miliyan 84,004,989.
5) Tanzania
Kasar Tanzania ce ke biye da kasar DR Congo a jerin kasashen da ke kan gaba wajen yawan al'umma, yawan al'ummar da ke kasar a yanzu sun kai miliyan 59,091,392
6) Afirka ta Kudu
Kasar Afirka ta kudu itace ta biyar kuma tana yawan al'ummar kasar ya karu daga miliyan 15,376,829 a 1955 zuwa 57,398,421 a 2018.
7) Kenya
Adadin al'ummar kasar kenya ya karu sosai daga miliyan 6,979,931 a shekarar 1955 zuwa miliyan 50,950,879 a shekarar 2018. Yawan al'ummar ya rubanya sau bakwai kenan.
8) Uganda
Adadin mutanen da ke Uganda ya karu daga miliyan 5,898,835 a shekarar 1955 zuwa miliyan 40,270,563 a shekarar 2018. Uganda na daya daga cikin kasashe masu tasowa a Afirka.
9) Algeria
Kasar Algeriya ce ta tara a jerin kasashen inda take da adadin al'umma miliyan 42,008,054.
10) Sudan
Daga Algeriya sai Kasar Sudan mai yawan al'umma 41,511,526 a shekarar 2018.
11) Morocco
Kasar Morocco ce ta 11 a jerin kasashen ke ke kan gaba wajen yawan al'umma, a halin yanzu akwai mutane miliyan 36,191,805 a kasar ta Morocco.
Maddallah! A yanzu mai karatu ya san kasashen ta suke kan gaba wajen yawan al'umma a nahiyar Afirka.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng