Da dumi-dumi: Yan bindiga sun kai farmaki ofishin yan sanda a jihar Kogi, sun hallaka hafsoshi 2
A yau Talata, 3 ga watan Afrilu wasu yan bindiga dadi sun far wa ofishin yan sanda da ke kauyen Gegu, hanyar Lokoja zuwa Abuja inda suka halaka yan sanda 2 da ke bakin aiki.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, William Aya, ya bayyanawa manema labarai cewa yan bindigan sun jikkata wani fursuna da ke tsare a ofishin kuma an kaishi asibiti.
Ya ce an gabatar da gawawwakin jami’an yan sandan dakin ajiye gawawwakin asibitin Federal Medical Centre, Lokoja.
Mr Aya ya ce an kaddamar da bincike cikin al’amarin da ya faru misalin karfe 2 na dare.
A bangare guda, wasu jama’an garin sun bayyanawa manema labarai cewa kimanin yan bindiga 5 ne suka zo a kan babur.
Daga zuwansu suka budewa ofishin yan sandan wuta inda suka kashe yan sanda 2 a take.
KU KARANTA: Hukumar sojin Najeriya ta tura dakarun soji na musamman jihar Zamfara
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng