Dumu-dumu: An kama wasu matasa suna sata a wani gida a Kano, duba hotunansu
Dubun wasu matasa biyu da suka haura wani gida domin yin sata a unguwar Danladi Nasidi dake a garin Kano ta cika.
An kama matasan ne yayin da suke tsaka da aikata mummunan sana'ar su ta sata. Matasan sun yi nasarar fito da wani inji dake zuko ruwa daga rijiya, watao sumo tare da kokarin sace tankin da ake tara ruwa a gidan.
Wasu mazauna unguwar ne suka dago yawar matasan kuma suka yi masu kwanton bauna har ta kai ga sun yi nasarar cafke matasan yayin da suke cikin gidan.
DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta gwangwaje matasan yankin Naija-Delta 90 da tallafin N500,000 ga kowannensu
Unguwar Danladi Nasidi tayi kaurin suna wajen samun yawaitar korafin sata. Mazauna unguwar kan koka kan cewar basa samun kwanciyar hankali duk lokacin da suka fita unguwa ko suka yi bulaguro.
Yawaitar sace-sace a unguwar bata tsaya kan tsallaka gidaje kadai ba, hatta ababen hawan mazauna unguwar basu tsira ba.
Yanzu haka an damka matasan hannun hukumar 'yan sanda domin zurfafa bincike da kuma matakin da ya dace.
Majiyar mu bata bayyana sunan matasan ko na maigidan da suka tsallakawa gida domin yin satar ba. Kazalika, majiyar bata ambaci ofishin hukumar 'yan sanda da aka mika matasan ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng