Ba zamu cigaba da karbar albashin N18,000 ba yayin da Sanata ke daukan miliyan N13.5m - Kungiyar ma'aikata

Ba zamu cigaba da karbar albashin N18,000 ba yayin da Sanata ke daukan miliyan N13.5m - Kungiyar ma'aikata

Ma'aikatan Najeriya, a karkashin hadaddiyar kungiyar masu aiki karkashin gwamnatocin daban-daban (AUPCTRE), ta ce ba zasu cigaba da karbar N18,000 a matsayin mafi karancin albashi ba yayin da kowanne Sanata ke karbar miliyan 13.5 duk wata, a matsayin kudin gudanarwa ba.

Shugaban kungiyar AUPCTRE, Kwamred Benjamin Anthony, da takwaransa na Abuja, Aliyu Maradun, sun bayyana rashin gamsuwa da yadda gwamnatin tarayya ke jan kafa a kan batun karin albashin ma'aikata.

Shugabannin sun ce har yanzu suna dakon sauraron karin da gwamnatin tarayya tace zata yi na albashi tun shekaru biyu da suka wuce.

KU KARANTA: Buhari ba zaiyi cacar-baki da Obasanjo ba saboda yana gaba dashi a aikin Soja - Femi Adesina

A taron da kungiyar reshen birnin tarayya, Abuja, ta gudanar, kwamred Maradun ya ce, "muna sane da irin tafiyar hawainiyar da batun karin albashi ke yi a kasar nan. An yi dokar karin albashi a shekarar 2011 da niyyar za a ke sabunta mafi karancin albashi duk bayan shekaru 5. Ya kamata a ce tun shekarar 2016 aka yi wani karin albashin. Tsawon shekaru biyu kenan an haramtawa 'yan Najeriya cin moriyar gumin aikinsu."

Kungiyar ta bukaci ma'aikatan kasar nan da su zama cikin shiri domin, a cewar kungiyar, karin albashin ba zai taba zuwa ta hanya mai sauki ba, ba tare da kungiyar ta tashi domin kwato hakkinta ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel