Kudaden da ake biyan Sanatoci na tafiyar lamuransu basu saba doka ba - Sanata Sabi
- Hukumar dake yankawa ma’aikata albashi ta kasa tace N13.5m da ake biyan sanatoci duk wata na tafiyar da lamuransu ba a kan ka’ida suke ba
- Hukumar tace albashi da alawus na kowane Sanata ya tsaya a N1.6 a ko wane wata
- Shugaban hukumar ya zagi masu yada labarai akan cewa sun eke fadar maganganu akan cewa an biyan Sanatocin kudade ba bisa ka’ida ba
Hukumar dake yankawa ma’aikata albashi ta kasa tace N13.5m da ake biyan sanatoci duk wata na tafiyar da lamuransu ba a kan ka’ida suke ba, amma sanatocin sunce hukumar bata fada haka ba masu yada labarai ne ke wannan ikirari.
Hukumar tace albashi da alawus na kowane Sanata ya tsaya a N1.6 a ko wane wata. Mai magana da yawun Sanatocin Aliyu Sabi Abdullahi (APC-Niger) yace kudin da suke karba bai sabawa ka’ida ba.
Shugaban hukumar ya zargi masu yada labarai akan cewa sune ke fadar maganganu akan cewa an biyan Sanatocin kudade ba bisa ka’ida ba.
KU KARANTA KUMA: Cigaban da Buhari ya kawo a fannin noman shinkafa kadai ya isa yasa a sake zabarshi - Lai Mohammed
Duk da cewa hukumar ta bayyana abunda ya kamata a ringa biyan Sanatocin, amma akwai kasafi da mukeyi wanda a bayyane yake kuma duk abunda muke karba bai sabawa doka ko ka’ida ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng