Wani ya hallaka yayansa da matar yayansa saboda abin duniya

Wani ya hallaka yayansa da matar yayansa saboda abin duniya

- Hukumar ‘Yan Sanda a jihar Ogun ta bayyana cewa ta kama wani, Okwudili Okoro bisa ga laifin kishe yayansa da matar yayan nasa

- Anyi nasarar kama Okoro ne sakamakon rahoto da aka samu daga bakin wani Joseph Nwagu wanda ya kawo a Ofishin ‘Yan Sanda cewa an kashe wasu ma’aurata

- Okwudili ya hallaka yayan sa ne saboda ya bi biyansa kudin sallama bayan ya shafe shekaru yana masa aiki a shagon siyar da kayan shafa

Hukumar ‘Yan Sanda a jihar Ogun ta bayyana cewa ta kama wani, Okwudili Okoro bisa ga laifin kashe yayansa da matar yayan. Hukumar tayi nasarar kama Okoro ne sakamakon rahoto da aka samu daga bakin wani Joseph Nwagu wanda ya kawo a Ofishin ‘Yan Sanda cewa an kashe wasu ma’aurata, Azuibike da matarsa Jacinta.

Wani ya hallaka yayansa da matar yayansa
Wani ya hallaka yayansa da matar yayansa

Babban Jami’in ‘Yan Sanda na Ofishin Sango, Nasirudeen Oyedele, ya jagoranci jamai’an hukumar zuwa wurinda abun ya auku inda suka kama wanda ake zargin, duk da cewa wanda suka aikata abun tare Kenneth, dan garin Abeokuta ya tayashi aikata wannan mummunan aiki.

KU KARANTA: Gwamna Shettima yayi tir da harin da aka kaiwa kauyukan Borno

Jami’in ‘Yan Sanda mai kula da hulda da jama’a, Abinbola Oyeyemi, yace bayan tuhumar wanda ake zargin dan jihar Ebonyi, ya bayyana cewa sun jima yana taya dan uwan nasa sana’ar kayan shafa na mata, da lokacin sallamarsa yayi sai ya fara kawo masa kabali da ba’adi.

Da yaga dan uwan nasa bashi da niyyar biyansa sai ya dauki hayar Kenneth, inda “suka siya addyna guda biyu suka nufi gidan mamacin, bayan sun tarar dashi yana cin abinci tare da matarsa kafin yace uffan suka hau kansa da matar tasa da sara har saida suka kashesu”, inji mai magana da yawun ‘Yan Sanda.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel