Mutane 3 da sunan su ke cikin barayin Najeriya sun fitar da kan su
- Kwanan nan ne Minista yada labarai ya fitar da sunayen wasu barayin Najeriya
- Akwai manyan mukarrabai da wadanda su ka rike mukami a lokacin Jonathan
- Wasu daga cikin wadanda ake zargi sun nuna cewa sharri ne ake yi masu kurum
Mun fahimci cewa jerin sunayen barayin kasar nan da Ministan yada labarai ya fitar ya jawo sabon surutu a halin yanzu. Wasu da-dama daga cikin wadanda aka ambata a jerin dai sun musanya cewa sun taba satar kudin Najeriya a baya.
Sanata Stella Oduah tace sharri kurum Gwamnatin nan ta ke yi mata da aka ce tana cikin wanda su ka wawuri dukiyar kasa. Shi ma dai Femi Fani-Kayode ya bayyana cewa kudin da ya kashe na yakin neman zaben Jonathan ba na sata bane.
KU KARANTA: FFK ya maidawa Lai Mohammed martani na cewa ya saci kudi
Shi kuwa Tsohon Gwamnan Neja Mu’azu Babangida Aliyu a karshen makon nan yayi barazanar maka Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a Kotu na sa sunan sa cikin barayin Najeriya inda yace bai taba satar ko kobo na dukiyar kasar ba,
Abin mamaki kuwa shi ne kwanakin baya Gidauniyar Martin Luther King na Amurka wanda ta ba Shugaba Buhari kyauta ta karrama tsohon Shugaban Hukumar fasa-kauri na kasa Abdullahi Dikko Inde wanda ake zargi da satar Naira Biliyan 40.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng