Najeriya da kasar Turkiyya zasu hada kai don karfafa hakar soji

Najeriya da kasar Turkiyya zasu hada kai don karfafa hakar soji

- Hadakar Gwamnatin kasar Najeriya data kasar Turkiyya sunce zasu hada kai domin habaka ayyukan sojin kasashen, jaridar gwamnatin kasar Turkiyya ce ta rawaito rahoton inda kasashe ta nuna yanda kasashen biyu suka yi yarjejeniya akan hakan

Wani dalibin jami'a yayi hade-haden kwayoyin da suka yi sanadiyyar rayuwar shi
Wani dalibin jami'a yayi hade-haden kwayoyin da suka yi sanadiyyar rayuwar shi

Hadakar Gwamnatin kasar Najeriya data kasar Turkiyya sunce zasu hada kai domin habaka ayyukan sojin kasashen, jaridar gwamnatin kasar Turkiyya ce ta rawaito rahoton inda kasashe ta nuna yanda kasashen biyu suka yi yarjejeniya akan hakan.

DUBA WANNAN: 2019: Saraki ya karyata jita-jitar fitowa takarar shi da ake yi

Kasashe biyun sun sanya hannu akan yarjejeniyar a birnin Ankara, inda sojojin Turkiyya dana Najeriya zasu hada kansu domin bayar da horo da kuma musayar dabarun yaki.

Cigaban da yarjejeniyar hadin gwiwar zai kawo sun hada da taimakawa dan Adam, yaki da ta'addanci, samar sa zaman lafiya ga al'umma, inganta ilimin harkar dabarun yaki ga sojoji, musayar ma'aikata da kuma inganta harkar atisaye.

Har ila yau zasu dinga yin musayar bayanan sirri da kuma budewa junansu ma'ajiyar tarihin soja, kawo cigaban ilimi da kuma bunkasa wajen ajiye kayan tarihi.

A cikin manyan darussan da za a baiwa sojojin akwai koyar dasu darasi akan shiga karkashin teku, yanda ake nutso mai zurfi, dabarun nemo abubuwan da aka dasa masu fashewa, da dai sauran su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng