Barayin Gwamnati: Babu wanda ya bani N1.6b da ake zargi na dashi - Mu'azu Babangida Aliyu
- A jerin sunayen da gwamnatin tarayyar ta fitar a satin daya gabata, ya nuna cewar akwai N1.6b wanda gwamnati ta alakanta su da tsohon gwamnan na Neja, sai dai kuma shi gwamnan ya musanta hakan, inda ya bayyana cewar shi babu wanda ya bashi wani kudi da ake alakanta shi dashi
Tsohon Gwamnan jihar Neja, Mu'azu Babangida Aliyu, yayi watsi game da zargin da gwamnatin tarayya take yi musu na cewar sune suka kwashe dukiyar Najeriya.
A jerin sunayen da gwamnatin tarayyar ta fitar a satin daya gabata, ya nuna cewar akwai N1.6b wanda gwamnati ta alakanta su da tsohon gwamnan na Neja, sai dai kuma shi gwamnan ya musanta hakan, inda ya bayyana cewar shi babu wanda ya bashi wani kudi da ake alakanta shi dashi. Saboda a lokacin da ake raba kudin an cire shi a cikin wanda za'a bawa kudaden saboda a lokacin yana daya daga cikin 'yan kungiyar G-7.
DUBA WANNAN: Kaduna: Baza mu yafewa duk wani dan kudancin Kaduna daya zabi El-Rufai ba - Inji tsohon kwamishina Mikaiah Tokwak
Tsohon gwamnan wanda ya gabatar da jawabin sa ta hanyar mai bashi shawara a fannin sadarwa, Mista Israel A. Ebije, a cikin wata sanarwa, ya ce: "Gwamnatin tarayya ta jawo hankalina a lokacin data sanya sunana a cikin jerin wadanda ake zargin su da handame dukiyar kasa, inda ake alakanta ni da cewar na karbi N1.6b daga ofis din tsohon mai bawa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro. Gaskiyar magana ita ce ban taba karbar wani kudi makamancin haka ba a lokacin mulkin Jonathan. A matsayina na daya daga cikin shugabannin G-7 ba ayi tunanin cewar zan amince da karbar kudin ba saboda hakane ma yasa ko tinkara ta ba ayi da zancen kudin ba."
Tsohon gwamnan ya bukaci gwamnatin tarayya data cire shi daga cikin jerin sunayen wadanda ake zargin, domin kuwa shi bashi da hannu a cikin wannan badakalar, inda ya kara da cewar 'yan Najeriya suna jirane suga gwamnati ta fitar da sunayen 'yan siyasa wadanda suke karkashin jam'iyyar APC wanda da yawa daga cikin su dasu aka ci kudin da ake tuhumar mu dashi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng