Barayin Gwamnati: Akwai makirci a cikin sunayen da gwamnatin tarayya ta fitar na barayin dukiyar kasa - Ferdinand Orbih

Barayin Gwamnati: Akwai makirci a cikin sunayen da gwamnatin tarayya ta fitar na barayin dukiyar kasa - Ferdinand Orbih

- Wani lauyan a jihar Benin, mai suna Ferdinand Orbih, ya zargi gwamnatin tarayya da yunkurin yin makirci akan sunayen mutanen da ta bayyana a matsayin barayin gwamnati

- Orbih ya ce, sunayen da gwamnatin tarayya ta fitar, akwai makirci a ciki, inda hakan ke nuna kodai gwamnatin tarayya bata da tabbacin da tsarin da kotu ta bayar a matsayin wadanda za'a bayyana a matsayin barayin gwamnati ko kuma dai gwamnati tana so ta nuna cewar tafi karfin doka

Barayin Gwamnati: Akwai makirci a cikin sunayen da gwamnatin tarayya ta fitar na barayin dukiyar kasa - Ferdinand Orbih
Barayin Gwamnati: Akwai makirci a cikin sunayen da gwamnatin tarayya ta fitar na barayin dukiyar kasa - Ferdinand Orbih

Wani lauyan a jihar Benin, mai suna Ferdinand Orbih, ya zargi gwamnatin tarayya da yunkurin yin makirci akan sunayen mutanen da ta bayyana a matsayin barayin gwamnati.

Orbih ya ce, sunayen da gwamnatin tarayya ta fitar, akwai makirci a ciki, inda hakan ke nuna kodai gwamnatin tarayya bata da tabbacin da tsarin da kotu ta bayar a matsayin wadanda za'a bayyana a matsayin barayin gwamnati ko kuma dai gwamnati tana so ta nuna cewar tafi karfin doka.

DUBA WANNAN: Ba laifi don mutum ya kare kanshi a lokacin da ake shirin cutar dashi - Shawarar da fadar shugaban kasa ta bawa 'yan Najeriya

A wata sanarwa daya bayar ga manema labarai a birnin Benin, Orbih ya ce bai kamata gwamnatin tarayya ta bayyana mutanen da kotu bata gama bincike akan su ba a matsayin barayin gwamnati. Orbih ya kara da cewar wadannan mutanen a halin yanzu basu da laifin komai har sai kotu ta gama bincike akan su tukunna za'a tabbatar da cewar suna da laifi ko basu dashi.

A sanarwar da yayi ya bayyana cewar gwamnatin tarayya bata fahimci abinda doka take ba ko kuma yanda doka take aiwatar da tsarin ta. Har yanzu ba a gama shari'a akan zargin da ake yiwa Nenadi Usman ba a kotu. Gwamnatin tarayya data saka ta a cikin jerin sunayen wadanda suka saci kudin kasa bata da wata hujja akan hakan.

"Hukuncin da gwamnatin tarayya ta dauka bai kamata da tsarin dimokuradiyya ba da kuma tsarin doka na kasar nan."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng