Da ace Shugaba Buhari ya san abin da yake yi da ba haka ba - Obasanjo
- Tsohon Shugaban kasa Obasanjo yace Gwamnatin Buhari ba ta da kan-gado
- Olusegun Obasanjo ya nuna Shugaban Kasa Buhari bai san inda ya dosa ba
- Sai dai wasu Jam’iyyar APC ta maidawa tsohon Shugaban kasar martani tumi
Mun samu labari cewa kwanan nan ne kuma tsohon Shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya kuma yin tir da Gwamnatin Buhari inda yace ba ta san abin da ta ke yi ba kuma ta gaza.
Olusegun Obasanjo ya kara nuna cewa da Jam'iyyar PDP da kuma ta APC mai adawa duk ba za su iya gyara kasar nan ba. Obasanjo ya nemi 'Yan Najeriya ka da su yarda da alkawuran APC da kuma tuban Jam'iyyar PDP.
KU KARANTA: An kama wasu masu addabar jama'a a Kaduna
Tsohon Shugaban kasar ya nunawa jama'a cewa ana neman a raba kan su ne da sunan addini da kabila domin manufar siyasa. Obasanjo yace da a ce wannan Gwamnati ta san inda ta sa gaba da abubuwa sun fi haka kyau.
Duk da haka dai Obasanjo yana ganin akwai wasu na gari a cikin APC da PDP. Sai dai Jam'iyyar APC mai mulki ta bakin Bolaji Abdullahi tace duk da kalubalen mulkin Kasar ba za ace Gwamnatin Buhari ta gaza gaba daya ba.
Ga dai bidiyon jawabin tsohon Shugaban kasar nan
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng