Wani abu sai yan siyasan Najeriya: Kalli yadda gwamna ta nade wando yana kwasar bola a Kebbi

Wani abu sai yan siyasan Najeriya: Kalli yadda gwamna ta nade wando yana kwasar bola a Kebbi

A ranar lahadin data gabata, 1 ga watan Afrilu ne dai aka hangi gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Atiku Bagudu yayin daya sa hannu cikin wani aikin gayyan tsaftace birnin Kebbi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

An yi wannan aiki da gwamnan ne a lokacin daya je ziyarar aiki a unguwar Nasarawa II dake Shiyar Sarakuna a Birin Kebbi, inda hukumar kula da tsare tsaren gidaje na jihar Kebbi ke gudanar da aiki.

KU KARANTA: Yan bindiga sun bindige mutane 2, sun yi garkuwa da wasu mutane 9 a Kaduna

A yayin ziyarar, gwamnan ya umarci ma’aikatar kasa da sifiyo da ta tabbata ta dauki leburori, da manyan motocin don tabbatar da an kwashe sharer gaba daya, tare da bude hanyoyin ruwa yadda ya kamata.

Wutar lantarki ta aika da wani mutumi lahira yayin da yake kokarin satar wayoyin lantarki
Bagudu

Bugu da kari, gwamnan ya yaba ma matasan unguwar Shiyar Sarakuna bisa kokarin aikin gayya da suka yi don tsaftace unguwanninsu, sa’anna ya sha alwashin basu dukkan gudunmuwar da suke bukata.

Wutar lantarki ta aika da wani mutumi lahira yayin da yake kokarin satar wayoyin lantarki
Gwamnan

Sai dai wasu masu tattauna al’amuran yau da kullum na ganin duk siyasa ce, musamman idan aka yi duba da cewa zabukan shekarar 2019 na karatowa, wanda akan samu yan siyasa na yin duk abinda zai ja hankalin jama’a akansu a irin wannan lokaci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng