Wani Matashi ‘Dan takara zai gwabza da Buhari a zaben 2019 a APC
- Adamu Garba ya shirya tsayawa takara da Shugaba Buhari a zaben 2019
- Matashin ‘Dan takarar yana sa ran doke Shugaban kasar idan ya fito zabe
- Yace idan ya hau mulki zai nemi shawarar tsofaffin da su ka ga jiya da yau
Mun samu labari cewa wani Matashi a Najeriya da ya kudiri niyyar zama Shugaban kasa zai gwabza da Shugaba Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki.
Adamu Garba wanda Matashi ne ‘dan shekara 35 ya bayyana cewa a Jam’iyyar APC zai tsaya takara a zaben 2019. Garba ya dauki shekara da shekaru yana shirin zama Shugaban kasar Najeriya ko da ba sananne bane a kasar.
KU KARANTA: Wani 'Dan Majalisa bai ji da dadi ba a Mahaifar sa
A cikin ‘yan kwanakin nan ne ‘Yan jarida su kayi hira da Adamu Garba a ofishin sa inda ya nuna cewa ba ya shakkar tika Shugaba Buhari da kasa a zabe mai zuwa. Garba yace yana da duk abin da ake bukata na Shugaba.
Garba ya bayyana cewa kafin mutum ya mulki Najeriya ya kamata ace yana da manufofi da kuma karfin aiwatar da hakan inda yace shi duk ya hada su. ‘Dan takarar yace idan su ka samu mulki za su nemi shawarar Dattawan kasar nan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng