Jerin ‘Yan kwallon da ba su taba karbar jan kati a fili ba har su kayi ritaya

Jerin ‘Yan kwallon da ba su taba karbar jan kati a fili ba har su kayi ritaya

Wannan karo mun koma harkar kwallon kafa ne inda mu ka kawo maku jerin wasu tsofaffin ‘Yan wasan kwallon kafa da tun da su ka fara taka leda har su kayi ritaya Alkalin wasa bai taba ba su jan kati ba.

Ga kadan daga cikin ‘yan wasan kamar yadda wani shafi na Sokkaa.com ya fara kawo su:

Jerin ‘Yan kwallon da ba su taba karbar jan kati a fili ba har su kayi ritaya
Har Ryan Giggs yayi ritaya bai taba samun jan kati ba

1. Ryan Giggs

Fitaccen ‘Dan wasan gaban Manchester United Giggs yayi rayuwar sa har ya gama bai san menene jan kati ba. Giggs yayi shekaru akalla 24 ana bugawa da shi a Manchester.

KU KARANTA: Diyar Dangote da sahibin ta su na shanawa a gefen ruwa

2. Alesandro Del Piero

Babban ’Dan wasan gaban Kasar Italiya ya fara buga kwallo tun 1994 kuma yayi ritaya ne a 2014 sai dai har ya gama rayuwar sa ba a taba ba shi jan kati ba a filin kwallo ko sau daya.

Jerin ‘Yan kwallon da ba su taba karbar jan kati a fili ba har su kayi ritaya
Lokacin da Van Der Sar yake faman tashe a Manchester

3. Edwin Van Der Sar

Haka kuma tsohon Golan kasar Holland, Van Der Sar bai taba ganin jan kati ba. Rikakken ‘Dan wasa mai tsaron gidan ya kuma bugawa Manchester United wasanni barkatai.

Bayan wadannan kuma akwai wasu fitattun ‘yan wasan da ba a taba jan kati ba. Akwai irin su Raul Gonzales da yayi kwallo a Birnin Madrid da dai sauran su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng