An damke wasu 'yan kungiyar asiri da ake dade a nema ruwa a jallo
- Hukumar ‘Yan Sanda tayi nasarar kama wasu mutane biyu da take zargin ‘yan kungiyar asiri ne, a jihar Legas
- An kamasu ne lokacin da suke kokarin kaiwa wasu ‘yan kungiyar adawarsu hari a unguwar Illasamajta, a jihar
- Hukumar tayi kira ga wadanda ke cikin irin wadannan kungiyoyi na asiri da su tuba, su bar wadannan kungiyoyi
Hukumar ‘Yan Sanda tayi nasarar kama wasu mutane biyu da take zargin ‘yan kungiyar asiri ne, a ranar Juma’a 30 ga watan Maris, a jihar Legas, Kanmi wanda akafi sani da Father, da Alami Samuel.
Mai magana da yawun hukumar ‘Yan Sanda, SP Chike Oti ya tabbatarwa manema labarai da cewa an kamasu ne a ranar Alahamis 29 ga watan Maris, lokacin da suke kokarin kaiwa wasu ‘yan kungiyar adawarsu hari a unguwar Illasamajta.
DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kama bindigogi 35 da alburusai 222 a jihar Nasarawa
Oti ya bayyana cewa, anyi nasarar kama Kanmi, bayan bayanai masu muhimmanci da suka samu akansa, wanda dama sun jima suna nemansa sakamakon laifukan da yake aikatawa a jihar, bayan umurnin da kwamishinan ‘yan Sanda Imohimi Edgar, ga jagoran ‘Yan Sandan dake unguwar Illasamajta, na kamo Father.
Kwamishinan Hukumar ‘Yan Sandan yayi kira ga wadanda ke cikin irin wadannan kungiyoyi na asiri da su tuba, su bar wadannan kungiyoyi kafin a kamasu a hukuntasu kamar yanda doka ta tsara.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng