Nigerian news All categories All tags
Kiranye: INEC sun yi kadan don sai na kammala wa’adi na zan dawo gida - Dino Melaye

Kiranye: INEC sun yi kadan don sai na kammala wa’adi na zan dawo gida - Dino Melaye

Sanata Dino Melaye yace Gwamna Yahaya Bello yayi barnar kudin sa a banza wajen yunkurin amfani da Hukumar INEC na yi masa kiranye don sai yayi shekaru 4 tun da al’ummar sa na son sa. Sanatan ya kuma yi karin haske kan wasu batutuwa da dama.

Sanata Dino Melaye na Jihar Kogi yayi hira da gidan jaridan VOA Hausa kwanakin baya inda ya bayyana cewa maganar cewa ya tsere daga kasar nan karyar banza ce kurum ake yadawa kuma Gwamna Yahaya Bello ne ke neman kashe shi.

Kiranye: INEC sun yi kadan don sai na kammala wa’adi na zan dawo gida - Dino Melaye

Dino Melaye yace Buhari mutum ne ba Annabi a don haka yana kuskure

An ga Sanata Dino Melaye a zaune cikin gidan sa inda yace babu abin da zai sa ya gudu ya bar ‘Ya ‘yan sa su kadai. Sanatan yace ba laifin sata yayi ba da ‘Yan Sanda za su har ya gudu. Yace kuma a nan gida za ayi duk wata shari’a ta kare.

KU KARANTA: Sanata Dino Melaye ya hurowa ‘Yan Sandan Najeriya wuta

‘Dan Majalisar ya kuma fadawa ‘Yan Sandan kasar cewa yana jiran su ko da su ke cewa za su zo su kama shi. Fitaccen Sanatan yace a lokacin babu wani sammaci da aka aiko masa daga Rundunar ‘Yan Sandan kasar sai dai kurum ya karanta a jarida.

Sanatan yace babu wanda ya isa yace ba ya son Shugaba Buhari wanda yace tamkar Uba yake a wurin Shugaba Buhari. Dino yace shi ne a sahun gaba wajen yakin neman zaben Shugaba Buhari amma dole ya fada masa gaskiya idan yayi kuskure.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel