Matsalar tsaro a Zamfara: Sanata Kabiru Marafa yayi kira da a tsige gwamna Adul-Aziz Yari

Matsalar tsaro a Zamfara: Sanata Kabiru Marafa yayi kira da a tsige gwamna Adul-Aziz Yari

Wani Sanata daga jihar Zamfara, Kabiru Marafa ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki irin matakin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya dauka a Jos, game da gwamnan jihar Zamfara.

Daily Trust ta ruwaito Marafa yace duba da sashi na 305 na kundin dokokin Najeriya na shekarar 1999, ya kamata Buhari ya dauki matakin tumbuke gwamnan jihar Zamfara Abdul-Aziz Yari, sakamakon damalmalewar harkar tsaro a jihar.

KU KARANTA: Ana murna bako ya tafi: Yan bindiga sun kai wani hari a Kaduna, sun kashe mutum 6

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sanatan ya cigaba da cewa kwatankwacin haka ne ya sanya Obasanjo a shekarar 2004 ya kaddamar da dokar ta baci a jihar Filato, tare da tsige gwamnan jihar na wannan lokaci, Joshua Dariye.

Matsalar tsaro a Zamfara: Sanata Kabiru Marafa yayi kira da a tsige gwamna Adul-Aziz Yari
Marafa

Obasanjo ya tumbuke Dariye ne sakamakon gazawarsa a wajen kawo karshen rikicin addini daya dabaibaye jihar Filao, inda ya nada Soja a matsayin gwamnan rikon kwarya, haka zalika Obasanjo yayi irin haka a jihar Ekiti, inda ya tsige Ayo Fayose a wancan lokaci. Amma Kotuna da dama sun haramta tumbuke gwamnoni

“Ina alhinin rayukan da aka kashe a jihar Zamfara, hare haren nan na wakana a kullum a jihar Zamfara, amma gwamatin jihar bata so taji ana magana game da hakan, ina kara kira da kaddamar da dokar ta baci a jihar Zamfara, a tsige gwamnan.” Inji Marafa.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu ya yi ga gwamnatin tarayya ta kara kaimi wajen kare rayukan al’ummma da dukiyoyinsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng