2019: Ya kamata Shugaba Buhari ya zarce Inji Shugaban YSFON
- Hukumar wasanni na Najeriya yana goyon bayan tazarcen Shugaba Buhari
- YSFON ta reshen Jihar Filato tace an aikin Gwamnatin Shugaba Buhari a fili
- Shugaban Hukumar yace Shugaba Buhari yayi kokari a harkar tattalin arziki
Hukumar wasannin Najeriya na reshen Jihar Filato watau YSFON tace abin da ya dace shi ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake fitowa takara a zabe mai zuwa na 2019 ganin irin ayyukan alherin da ya kawowa Najeriya a mulkin sa.
Kamar yadda labari ya zo mana daga Jaridar nan ta Daily Trust, an yi wannan kira ga Shugaban kasar ne a cikin makon nan. Hukumar wasannin tace ya kamata Shugaban kasa Buhari ya dabbaka ayyukan da ya shiryawa Najeriya.
KU KARANTA: Wani Bawan Allah ya sa kudi ga wanda ya kawo masa ayyukan Buhari
Shugaban Hukumar YSFON yace Shugaba Buhari ya gama fitar da tsarin da za ayi amfani da shi wajen ganin an kai ga ci don haka Hukumar tace akwai bukatar Shugaban kasar ya kammala wannan aiki da ya fara na cigaban kasa.
Idris Salihu Kwando wanda shi ne Shugaban YSFON yayi hira da Daily Trust a Garin Jos. Kwando yace an ga aikin wannan Gwamnati a fili musamman a bangaren tattalin arziki da yaki da rashin gaskiya don haka kurum ya sake fitowa zabe
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng