Rikicin manya: Buratai ya mayar ma TY Danjuma raddi game da kisan Sojoji

Rikicin manya: Buratai ya mayar ma TY Danjuma raddi game da kisan Sojoji

A ranar Alhamis, 29 ga watan Maris ne rundunar Soji ta daya ta gudanar da binne Sojojinta guda 11 da yan bindiga suka kashe su a garin Birnin Gwari na jihar Kaduna, kamar yadda NAIJ.cm ta ruwaito.

Sojojin da aka yi ma jana’iza a jiyan sun hada da Bamidele Adekunle, Christian Ogochukwu, Adam Muhammad, Sulaiman Mubarak, Bashir Sani, Usman Abubakar, Nafiu Iliyasu, Sufaynu Ahmad, Alhassan Ibrahim, Abegunde Emmanuel da Hammed Olubode.

KU KARANTA: Ba zamu taba mantawa da badakalar cin hanci da rashawa da ya gudana a zamanin Goodluck ba – Osinbajo

Sai dai a yayin binne Sojojin, babban hafsan sojan kasa, Laftaar janar Tukur Yusuf Buratai yayi wata magana, jurwayi mai kamar wanka, ko kuma ace hannunka mai sanda zuwa ga tsohon babban hafsan Sojan kasa na Najeriya, TY Danjuma.

Rikicin manya: Buratai ya mayar ma TY Danjuma raddi game da kisan Sojoji
Buratai

Buratai, wanda ya samu wakilcin kwamandan runduna ta daya dake Kaduna, Manjo janar Muhammad Muhammad ya bayyana alhinin kisan Sojojin, wanda yace dukkaninsu, banda Hammed, basu shekara a aikin Soja ba, amma ga shi har sun sadaukar da rayukansu.

“Don haka ya za’ayi wani mutum kuma ya dinga zargin Sojoji da hada kai da abokan yakinsu? Idan har mutum zai yi magana, sai ya san abinda zai dinga fada, ba ya dinga yin kudin goro ba.” Inji shi, a wani raddi da yayi ga TY Danjuma, wanda ya zargi Sojoji da hada kai da mahara makiyaya a Taraba.

Majiyar Legit.ng ta ruwato Buratai daga karshe ya dauki alwashin hukunta duk masu hannu cikin wannan kisan da aka yi ma Sojoji, inda yace: “Jininsu bai zuba a banza ba, mu da muka rage, zamu cigaba daga inda suka tsaya, zamu cigaba da aikinmu yadda ya kamata.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng