Jawabin Shugaba Buhari jiya a Legas wajen taron bikin Bola Tinubu
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jawabi wajen babban taron da aka shiryawa tsohon Gwamnan Jihar Legas Bola Tinubu wanda ya cika shekaru 66 a Duniya.
Ga tsokaci daga cikin bayanin Shugaban kasar:
1. Ina matukar taya aboki na kuma abokin tafiya watau Bola Tinubu murnar wannan rana. Sai dai zama rikakekken ‘dan siyasa babu manufar kwarai bai da amfani.
2. Tinubu ya sha ban-bam da sauran ‘yan siyasa. Tinubu mutum ne mai neman ganin cigaba a al’umma ta fannin tattalin arziki da sauran bangarori.
3. Na yabawa Mataimaki na Farfesa Yemi Osinbajo da sauran ire-iren sa da su ka ka kirkiro wannan abu domin Bola Tinubu.
KU KARANTA: Shugabannun kasar Najeriya daga 1999 zuwa yau
4. Mu na kokari ne mu kawo gyara a madadin barna da kuma tsaro a madadin tashin hankali sannan kuma mu maye gurbin arziki da talauci.
5. Ya zama dole mu yi kokarin gina al’umma su zama mutane. A matsayin mu na masu addini, mun san cewa gaba ta fi baya yawa.
6. Mu na kokarin mu gyara kasar nan ne daga ginin banzan da aka yi mata, a mu daura ta a kan turba ta kwarai a halin yanzu.
7. Kokarin mu shi ne kowane Yankin kasar nan da bangare su hadu domin a taimaki juna ta fuskar tattali da siyasa.
8. Mun kawo tsarin da za su taimakawa mutanen Kasar nan; daga ciki akwai kudi da mu ka narka a harkar gona.
9. Sai mu hada kai domin ganin Kasar mu Najeriya ta cigaba ta kuma fi da.
10. Ina taya aboki na Asiwaju murnar wannan rana ta yau a Duniya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng