Nigerian news All categories All tags
Muhimman abubuwa 10 daya dace ka sani game da Bola Tinubu yayin cikar sa shekaru 66 a duniya

Muhimman abubuwa 10 daya dace ka sani game da Bola Tinubu yayin cikar sa shekaru 66 a duniya

- Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Shugaban jam’iyyar APC, yana daya daga cikin gwarzayen Najeriya

- Tarihin Najeriya na wannan karni bai zai taba cika ba tare da ambaton sunan tsohon gwamnan jihar Legas ba din ba

- Duk da adawar dake tsakanin su amma sai gashi gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, yace, jagoran jam’iyyar ta APC ya zama katanga abin jingina a kasar Yarabawa

- Akwai wasu masu ganin cewa ma kwarjinin siyasar Bola Tinubu ta dara na tsohon gogagen dan siyasar kasar Yarabawa marigayi Cif Obafemi Awolowo

Yau Alhamis 29 ga watan Maris, ranar farin ciki ce ga a cikin rayuwar jigo a siyasar Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu. Iyayen jigon na jam'iyyar APC ba su taba tsamanin cewa dan nasu zai zama mashahurin dan siyasa ba ranar haihuwar sa a ranar Talata 29 ga watan Maris na 1952.

Shigowar Tinubu cikin harkar siyasa a Najeriya ya kawo muhimman canje-canje tun bayan kafa jam'iyyar APC. Ko kana sonsa ko baka sonsa, akwai abubuwa masu muhimmanci daya kamata ka sani game da wannan shahararren dan siyasa daya cika shekara 66 a yau.

Muhimman abubuwa 10 daya dace ka sani game da Bola Tinubu yayin cikar sa shekaru 66 a duniya

Muhimman abubuwa 10 daya dace ka sani game da Bola Tinubu yayin cikar sa shekaru 66 a duniya

1. Ilimi

Bola Tinubu yayi makarantar primary ta St John a jihar Legas, sai makarantar Children’s Home a Ibadan. Bayan nan ya koma Richard Daley College, Chicago, Illinois, daga nan kuma sai Jami’ar Chicago, duka a kasar Amruka. Ya samu takardar digiri a fannin kasuwanci a shekarar 1979.

2. Nasarorin da ya samu a fannin Ilimi

Tsohon gwamnan jihar Legas ya zamanto gaba gaba a fannin karatu, kuma ya saba karbar lambar yabo ta dalibai masu hazaka, sakamakon haka ya samu kulawar gwamnati da takardar girmamawa a fannin lissafi da ajiya, bayan ya samu maki 3.54 a cikin 4.0 da ake bukata.

KU KARANTA: Sanatocin jihar Kaduna sunyi wa El-Rufai kafar ungulu a kan ranto $350m

3. Horo a fannin Aiki

Shugaban jam’iyyar APC na tarayya yayi aiki da Arthur Anderson da Deloitte and Sells, sai GTE Services Corporation. Yayi aiki da Mobil Oil na Najeriya, a 1983.

4. Siyasa

Ya shiga siyasa a cikin 1990s. Ya shiga jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), inda ya lashe tikitin farko na jam’iyyar don yayi takara a zaben majalisar wakilai a yammacin jihar Legas, wanda ya lashe zaben ya kayar dan jam’iyyar adawa na National Republican Convention (NRC).

5. Abunda ya fuskanta lokacin gwamnatin IBB

Anci mutuncin Tinubu kuma an kama shi lokuta da dama, bisa ra’ayinsa daya bambanta dana gwamnatin. Yana yawan maganganu na suka ga gwamnatin.

6. Gwagwarmayar da yayi lokacin gwamnatin Abacha

An tursasashi har yayi hijira ya bar Najeriya saboda yawan kai masa hari da akeyi ana kokarin kashe shi. Bayan ya tafi hijira ya shiga kungiyar NADECO, tare da wasu masu sukar mulkin Abacha. Daganan ne masu goyon bayan kungiyar tare da Tinubu suka bude gidan Radio na Kudirat, wanda ya zama karfen kafa ga gwamnatin Abacha.

7. Rayusar a matsayin Gwamna

Tinubu ne gwamna na uku da ya mulki jihar Legas ta siyasance, a jam’iyyar AD, bayan da soji suka mayar wa farar hula mulki a 1999. Yayi mulki har sau biyu. Ya taimaka ta bangaren samar da kudin haraji na gida (IGR), a jihar, wanda ake samu ya koma biliyoyin naira.

8. Daliban Tinubu a makarantar Siyasa

Mutanen da jigon siyasa na Yarabawa ya horas sunada yawa. Sun hada da; Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasa a Najeriya; Babatunde Raji Fashola, Ministan Lantarki, Ayyuka da Gidaje kuma tsohon Gwamnan jihar Legas, Rauf Aregbesola, gwamnan jihar Osun, da sauransu.

9. Shafe tarihin Chief Obafemi Awolowo na siyasa

Duk da cewa Awolowo ya taimaka wajen habbaka kasar Yarabawa, ta hanyar bayar da ilimi kyauta, lokacin da yake Prime Minista na Yankin Yammacin kasa a shekarun 1950s. Tinubu shine dan siyasa na farko cikin Yarabawa wanda jam'iyyar sa ta kayar da gwamnati mai mulki hakan kuma ya sa dole ake dama wa dashi a harkokin gwamnati.

10. Gujewa zagon kasa na jam’iyyar PDP

A lokacin da sauran gwamnoni na jam’iyyar AD suka rasa kujerunsu bayan PDP ta lashe zabe, Tinubu ne kadai ya koma kan kujerarsa ta hanyar ayyukan da ya gudanar a jiharsa a shekarar 2003, ya kasance gwamna mai mulki dan jam’iyyar AD a gaba daya jihohi 36 na fadin kasar nan.

Hakan bai hanashi kwarin gwiwa ba a fannin siyarsa, inda ya hada kai da sauran ‘yan jam’iyyu masu ra’ayi irin nasa don su canza lamurran siyasa. A cikin shekaru kadan shi da wasu ‘yan siyasa suka hada jam’iyyar ta APC, wadda a yanzu take mulkin jihohi 22 a fadin kasar nan.

Saboda kwarewa ga gogewarsa a siyasa ne ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin jagoran kwamitin sulhu tsakanin yan jam'iyyar APC don tunkarar zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel