Faduwar jarabawar WAEC: Majalisa ta bukaci Ministan Ilimi ya bayyana a gaban ta

Faduwar jarabawar WAEC: Majalisa ta bukaci Ministan Ilimi ya bayyana a gaban ta

- Majalisar Dattijai ta koka game da yawan faduwa jarabawar gama makarantar sakandire na WAEC

- Ta bukaci ministan Ilimi na kasa, Malam Adamu Adamu da yazo Majalisar yayi mata bayani a kan abunda ke faruwa

- Ministan zai fuskanci Majalisar ne tare da shugaban hukumar jarabawar ta WAEC tare da wani cikin masu ruwa da tsaki a kan lamarin

A ranar Laraba 27 ga watan Maris ne majalisa ta bukaci Malam Adamu Adamu, Ministan Ilimi na kasa da yazo gabanta domin yayi mata bayani a kan makasudin yawan faduwar jarabawar gama makarantar sakandire WAEC da yara keyi a kasar nan.

Ana sa rai cewa Adamu zai yiwa kwamitin kula da harkokin Ilimi na Majalisa bayanin abin ke janyo yawan aukuwar hakan, kuma ya bayyana mata mafitar da za’a bi don magance sake aukuwar wannan matsalar. Kwamitin za su gabatar wa majalisa bayanin binciken da sukayi nan da wata daya.

Faduwar jarabawar WAEC: Majalisa ta bukaci Ministan Ilimi ya bayyana a gaban ta
Faduwar jarabawar WAEC: Majalisa ta bukaci Ministan Ilimi ya bayyana a gaban ta

KU KARANTA: Yiwa 'yan Boko Haram afuwa ya nuna cewa ba'a ci gallabar su ba - Fasehun

Legit.ng ta gano cewa Sanata Umaru Kurfi ya kawo korafi a zaman majalisa a ranar Laraba 28 ga watan Maris, wanda yayiwa lakabi da “Bukatar bayani akan yawan faduwar jarabawar gama makarantar sakandare. Tun shekara ta 2009 da tara aka fara samun irin wannan mummunar faduwar jarabawa, wanda abun kunya ne da damuwa ga kasar nan da kuma iyayen yara baki daya.

A ranar Talata, 13 ga watan Maris, Legit.ng ta ruwaito cewar, hukumar jarabawar ta WAEC, ta bayyana sakin jarabawar gama sakandire ta watan Janairu/Febrairu na 2018.

Babban sakataren majalisa, Olu Adenipekun, wanda ya sanar da sakin jarabawar a Legas, yace an rike sakamakon yara 1,021, an rike sakamakon jarabawar yaran ne bisaga korafe korafe da aka samu na satar ansa a lokacin rubuta jarabawar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164