Najeriya zata fara aro kudi a bankin Musulunci domin gujewa biyan kudin ruwa

Najeriya zata fara aro kudi a bankin Musulunci domin gujewa biyan kudin ruwa

- Daraktan Kudi na Najeriya, Alhaji Aliyu Ahmed, ya bayyana cewar gwamnati zata mayar da hankali wajen karbo kudade daga manyan bankunan Musulunci domin kaucewa biyan kudin ruwa

- A yanzu haka dai Najeriya tana da bankin Musulunci daya ne rak wanda ake kira Ja'iz Bank, wanda aka yi masa rijista domin gudanar da aiki a shekarar 2016

Najeriya zata fara aro kudi a bankin Musulunci domin gujewa biyan kudin ruwa
Najeriya zata fara aro kudi a bankin Musulunci domin gujewa biyan kudin ruwa

A wani bayani da aka aika wajen babban taron habaka harkokin kasuwanci da kudi na musulunci, Ministar kudi ta Najeriya Mrs. Kemi Adeosun, tace musabbabin hada tarin shine domin a tattauna da kuma gano hanyoyin da za a dinga samun kudaden shiga saboda gudanar da ayyukan cigaba a kasar nan, sannan kuma ana so a gano hanyar da za abi domin a kaucewa basuka wadanda suke dauke da kudin ruwa.

DUBA WANNAN: Kunji wani shi kuma: Yana garkuwa da mutane domin ya kara jarin shagon sa

Daraktan Kudi na Najeriya, Alhaji Aliyu Ahmed, wanda ya wakilci Ministar kudin a wurin taron, ya bayyana cewar gwamnati zata mayar da hankali wajen karbo kudade daga manyan bankunan Musulunci domin kaucewa biyan kudin ruwa.

Hakan wata hanyace da bankuna Musulunci zasu samu damar yin harka da manyan bankunan Musulunci na kasashen duniya domin samar da cigaba ga al'umma, a bayanin Alhaji Garba Imam, shugaban wani babban kamfani da yake hada-hadar kudade na Islama dake cikin birnin Abuja.

A yanzu haka dai Najeriya tana da bankin Musulunci daya ne rak wanda ake kira Ja'iz Bank, wanda aka yi masa rijista domin gudanar da aiki a shekarar 2016.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng