Dara taci gida: Trump zai gurfana a gaban kotu

Dara taci gida: Trump zai gurfana a gaban kotu

- Ana tuhumar shugaba Donald Trump da yin amfani da kujerar sa ta shugaban kasa wurin tara kudade masu tarin yawa a kamfanonin sa

- Babban alkalin yankin jihar Maryland dake kasar Amurka ya bukaci da a iza keyar Shugaban kasar Amurkan Donald Trump gaban kuliya

- Akwai yiwuwar cewar, idan har aka tabbatar da cewar laifukan da ake zargin shi dasu suka zama gaskiya to zai iya rasa kujerar sa ta shugabancin kasar Amurka

Dara taci gida: Trump zai gurfana a gaban kotu
Dara taci gida: Trump zai gurfana a gaban kotu

Babban alkalin yankin jihar Maryland dake kasar Amurka ya bukaci da a iza keyar Shugaban kasar Amurkan Donald Trump gaban kuliya, saboda zargin sa da ake da aikata laifin almundahana, inda ya hada kai da kasar Rasha ya lashe zaben da aka gabatar a shekarar 2016.

DUBA WANNAN: Jihar Benuwe: Cacar baki yasa tayi wa saurayinta yankan rago

Alkalin ya ce laifin da shugaba Donald Trump yayi ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar Amurka, inda Trump yaje ya karbi kudade daga hannun gwamnatocin wasu kasashen ketare.

Lamarin shugaba Trump din ya fito fili ne a yayinda ake binciken takardun lissafin dukiyoyin kasashen waje da suke kamfanonin shugaba Trump din dake birnin Washington da Maryland.

Ana tuhumar shugaba Donald Trump da yin amfani da kujerar sa ta shugaban kasa wurin tara kudade masu tarin yawa a kamfanonin sa.

Bayan haka kuma ana zargin shugaban kasar ta Amurka da hada baki da kasar Rasha wurin taimaka mashi yaci zaben da aka gabatar a shekarar 2016, sannan ana zargin shi da aikata laifin almundahana da kuma kula haramtacciyar alaka da wata mata mai suna Stephanie Clifford tun a shekarar 2006, da dai sauran wasu manyan laifuka daya aikata.

Akwai yiwuwar cewar, idan har aka tabbatar da cewar laifukan da ake zargin shi dasu suka zama gaskiya to zai iya rasa kujerar sa ta shugabancin kasar Amurka.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng