Yadda wani karamin Yaro ya tsallake rijiya da baya a hannun masu yankan kai a birnin Kebbi

Yadda wani karamin Yaro ya tsallake rijiya da baya a hannun masu yankan kai a birnin Kebbi

Wata mahaifiyar mai suna Hajiya Salamatu Kaoje ta bayyana yadda Yaronta mai karancin shekaru ya tsallake rijiya da baya daga hannun wasu masu yankan kai a jihar Kebbi, kamar yadda Legit.ng ta jiyo.

Salamatu ta bayyana haka ne cikin wani shirin gidan rediyon Alheri rediyo dake jihar Kaduna, Yanayin gari, inda tace masu yankan kan sun saci yaron nata ne a satin daya gabata, inda suka kai shi katafaren gida.

KU KARANTA: Babbar magana: Yansanda 13 ne suka taimaka ma yaran Dino Melaya da suka tsere daga Ofishin Yansanda

Yaron ya bayyana ma mahafiyarsa cewa ya ga kananan yara da dama a gidan, daga ciki har da wata karamar yarinya da bata fi shekaru 3 ba, don kuwa tana sanye da kunzugun famfas, ya kara da cewa duk magiyar da yayi ga mutanen da suka sato shi bai sa sun sake shi ba.

Bayan wani lokaci sai mutanen suka mika shi ga wani mutumi da ya shigo gidan, wanda ya basu kudi naira dubu dari da hamsin, N150,000, inda suka nemi ya kara musu kudi, don kuwa babu yadda za’ayi ya biyasu N150,000 akan kananan yara, kuma ya basu hakan akan yaro mai shekaru 15.

Daga nan ne sai mutumin ya kara musu naira dubu biyar, ganin haka Yaron ya kwala ihu, inda suka buga masa karfe a kafa don yayi shiru. Yaron yayi yunkurin tserewa daga gidan, amma yaran da ya tarar a gidan suka fada msa su kam ba zasu iya ba, don a kwanakin baya wani dan uwansu yayi yukurin tserewa, amma da suka kama shi, a gabansu suka kashe shi, don haka idan ya tsere ya shaida ma iyayensa a kawo musu dauki.

Da take fadin yadda Yarin ya tsere kuwa, cewa ta yi ya mamayi maigadin gidan ne a lokacin da ya sha giya yayi tatil, inda ya bude gate din gidar, ya zura a guje, inda ya fada cikin wasu almajira bayan gudu mai nisa, inda suma suka fatattake shi, daga bisani kuma ya hadu da yan banga, inda ya kwana a wajensu, suka kai shi gida da safe.

Bayan hankalin yaron ya samu, ya tabbatar da cewar wannan gidan na tsohon garin birnin Kebbi ne, amma ba zai iya cewa ga inda yake ba a yanzu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng