Oyegun: Maganar Shugaba Buhari ba hujja bace inji Lauyan da ke kare APC a Kotu

Oyegun: Maganar Shugaba Buhari ba hujja bace inji Lauyan da ke kare APC a Kotu

An maka Jam'iyyar APC mai mulki a Kotu idan ba ku manta ba a dalilin karawa Shugabannin Jam'iyyar wa'adi wanda wasu 'Ya 'yan APC ke ganin ya sabawa ka'idar dokar kasa da kuma tsarin Jam'iyya.

Jam'iyyar ta fara kare kan ta a babban Kotun Tarayya da ke Abuja jiya kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust. Wadanda ake kara a Kotu su ne Shugaban Jam'iyyar John Oyegun da Sakataren gudanarwa Osita Izunaso.

Oyegun: Maganar Shugaba Buhari ba hujja bace inji Lauyan da ke kare APC a Kotu
Lauyan APC ya nemi ayi watsi da maganar Buhari

Lauyoyin da ke kare Jam'iyyar sun nemi karin lokacin kafin a fara shari'ar inda masu karar ke gani kurum a soma saboda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna cewa matakin da aka dauka bai halatta ba a taron APC na makon nan.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta gyara wasu hanyoyi a Kudancin Najeriya

James Daudu wanda yana cikin masu kare APC yace matsayar da Shugaban kasa yake a kai ba hujja bace illa kurum ya fadi ra'ayin sa ne. Babban Lauya yace sai Jam'iyya sun zauna sub dauki mataki tukuna za a yi la'akari da wata magana.

Alkali Nnamdi Dimgba yayi alkawarin yin adalci inda ya dage karar zuwa tsakiyar watan gobe na Afrilu. Wadanda su ka kai karar Jam'iyyar sun hada da Sani Mayanchi da Machu Tokwat wanda duk manyan ne a Jam'iyyar ta APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng