Gwamnatin Tarayya za ta bada kwangilar wani hanya daga Garin Legas zuwa Shagamu

Gwamnatin Tarayya za ta bada kwangilar wani hanya daga Garin Legas zuwa Shagamu

- Za a bada kwangilar titin Garin Shagamu har zuwa cikin Ikorodu

- Wannan aikin zai ci makudan kudi har sama da Naira Biliyan 20

- Gwamnatin Buhari tace yin titin zai taimaka wajen safara a Yankin

Dazu nan ne a taron Majalisar zartawa na kasar watau FEC Gwamnatin Tarayya ta amince da kwangilar wata hanya a Garin Legas da Ogun. Za a kashe sama da Naira Biliyan 20 wajen wannan aiki kamar yada mu ka samu labari.

Gwamnatin Tarayya ta bada kwangilar wani hanya daga Garin Legas zuwa Shagamu
Shugaban kasa Buhari zai bada kwangilar hanyar Shagamu

Gwamnatin Buhari za ta sa hannu kan kwangilar titin Ikorodu zuwa Sagamu wanda zai ci Naira Biliyan 20.8 kamar yadda Ministan yada labarai da al’adu na kasar Lai Mohammed ya bayyanawa manema labarai a ofishin Shugaban kasa.

KU KARANTA:

A yau Laraba Ministocin Shugaba Buhari su ka yi taro na kusan sa’a 5 inda Ministan sufurin jirgin sama Hadi Sirika ya bayyana cewa Shugaban kasa ya amince da ware wasu Biliyan 4.3 na wasu gyare-gyare a Makarntar tukin jirgi na Zaria.

A taron kuma Ministocin ilmi da sadarwa Mista Solomon Dalung da Malam Adamu Adamu sun bayyanawa Gwamnatin Shugaban kasa Buhari irin kokarin da su kayi daga hawan su ofis zuwa yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng