Barka: Koriya ta Arewa zata dakatar da shirin samar da makaman kare dangu da ta sa a gaba

Barka: Koriya ta Arewa zata dakatar da shirin samar da makaman kare dangu da ta sa a gaba

Matashin shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jun-Un ya tabbatar ma Duniya cewar kasarsa a shirye take ta yi watsi da shirinta na sarrafa makamin kare dangi, wato Nukiliya, matukar kasar Amurka da China zasu samar da yanayin zaman lafiya ingantacce.

Kim ya bayyana haka ne a wani ziyarar ba zata da ya kai zuwa kasar China a ranar Talata 27 ga watan Maris, ziyararsa ta farko zuwa wata kasar waje tun bayan darewarsa mukamin shugaban kasa, inji rahoton BBC Hausa.

KU KARANTA: Yadda yan Boko Haram suka saci wata mace mai ciki har ta haihu a hannunsu, suka rada ma yaron suna

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yayin gawanar tasu, shugaban kasar China, Xi Jinping ya fada ma Kim cewa kasar China na nan kan matsayarta na raba yankunan Koriya da makaman Nukilya.

Barka: Koriya ta Arewa zata dakatar da shirin samar da makaman kare dangu da ta sa a gaba
Kim da Xi

Wadannan maganganu da suka fito daga bakunan shuwagabannin biyu na alanta kyakkyawar zato da ake yin a cewar kasar Koriya ta Arewa zata yi watsi da shirin samar da Nukiliya ba tare da an kai ga baiwa hammata iska ba.

A nasa bangaren, Christopher Hill, tsohon mai shiga tsakani akan shirin mallakar Nukiliya na Koriya ta Arewa, ya bayyana wannan ganawa tsakanin shuwagabannin biyu a matsayin abu mai muhimmanci.

“Gwamnatin kasar Sin ta nuna ma Kim cewar ba zasu yi maraba da shi ba, har sai ya koma turbar aniyar yin watsi da shirin mallakar makaman kare dangi, don haka a yanzu ana sa ran Kim zai bayyana ma shugaban kasar Amurka manufarsa ta yin watsi da makaman Nukili, a wata haduwa da ake sa ran zasu yi.” Inji Hill.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng