Wata mata ta shafe shekaru 25 ta na jinyar mijin ta a kasar Saudiya ba tare da gajiyawa ba

Wata mata ta shafe shekaru 25 ta na jinyar mijin ta a kasar Saudiya ba tare da gajiyawa ba

A yayin da al'ummar duniya ke yada irin girmamawa, lambar yabo gami da soyayyar da suke yiwa iyayen su mata a dandalan sada zumunta domin tunawa da ranar iyaye mata, wani mutum ya yada abinda ya sanya mutane da dama hawaye.

Wannan Balarabe na kasar Saudiya, Hattan Asali, ya yi jinjina ga mahaifiyar sa a shafin sa na twitter sakamakon shafe shekaru 25 da tayi zaune a gefen gadon mahaifin sa tana jinyar sa ba tare da kosawa ba.

Hattan a shafin sa ya bayyana cewa, 'yan kalilan ne suke da masaniyar rashin lafiyar mahaifin sa ta yadda ba iya motsa kowace gaba a jikin sa inda ko numfashi da cin abinci sai da taimakon injinan asibiti ya ke samun dama.

Mahaifiyar Hattan a gefen gadon mahaifin sa tare da rubutun da ya yada a shafin sada zumunta
Mahaifiyar Hattan a gefen gadon mahaifin sa tare da rubutun da ya yada a shafin sada zumunta

Mahaifiyar Hattan dai ta shafe tsawon shekaru 25 ta na dawainiya ga mijin ta baya ga kulawa da 'ya'yan ta wanda yanzu ya kawo tana kuma hadawa da jikoki.

KARANTA KUMA: Na shafe fiye da shekaru 10 ba tare da kusantar iyali ba - Fasto

Hattan dai ya sanya hoton mahaifin sa tare da mahaifiyar sa zaune a gefen gadon da take dawainiya, wanda wannan lamari ya sanya al'umma da dama cikin kwalla da zubar da hawaye, yayin da wasu suka gaza cewa kamai domin girman wannan abun al'ajabi.

Da yawan mutane sun yi son barka tare da lambar yabo kan mahaifiyar Hattan, tare da watso addu'o'in su ga mahaifin sa na neman waraka.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, bincike ya bayyana yadda lahani na hayakin igiyar leko ya yiwa na karan sigarin fintinkau.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel