An gano waye mutumin da harin makami mai linzami ya hallaka a kasar Saudiyya
A ranar 26 ga watan Maris na 2018 , mayakan kungiyar Houthi sun harba bama-bamai guda bakwai zuwa birane da dama a kasar Saudiyya musamman garuruwan da ke dauki da al'umma da yawa.
Garuruwa da aka chila bama-baman sun hada da babban birnin Saudiyya Riyadh, Birnin Khamis, Mushait, Jizan da kuma Najran sai dai dakarun sojojin kasar ta Saudiyya sunyi nasarar lalata bama-baman kafin su sauka a biranen da aka aike da su.
Rahotanni daga kafar yadda labarai na Al Arabiya sun bayyana cewa birbishin bam din da aka jefa birnin Riyadh ya fada kan wani gida inda yayi sanadiyar rasuwar wani mutum mai suna Abdelmontaleb Ahmad Hussin Ali wanda asalin sa dan kasar Misra ne amma yana aiki a kasar Saudiyya.
Burbushin bam din ya sauka ne a rufin gidan da ya ke zaune a yayin da yake cin abinci tare da dan uwansa da abokin sa a daren Lahadi da ta gabata. Nan take Abdelmontaleb ya ce ga garin ku, an kuma garzaya da dan uwansa da abokin sa asibiti don yi musu magani sakamakon munanan raunukkan da suka samu.
KU KARANTA: Sauya jadawalin zabe: An bayyana sunayen ‘yan Majilasar Dattawa masu goyon bayan Buhari
Jim kadan bayan rasuwar sa, an sanar da ofishin jakadancin kasar Misra da ke Saudiyya don ta fara shirye-shiryen tafiya da gawarsa kasar na Misra don yi masa jana'iza. Saudiyya ta mika ta'aziyar ta ga kasar ta Misra da kuma iyalen mamacin yayin da ake yiwa wadanda suka jikkat fatan samun lafiya.
Mai magana da yawun kasashen labarabawa, Turki Al Malki ya goyon bayan da gwamnatin Iraqi ke bawa kungiyoyin yan ta'adda ta hanyar tallafa musu da makamai masu lahani abin damuwa ne kwarai da gaske.
Wannan dai ba shine karo na farko da yan kungiyar na Houthis ke yunkurin kai hari a biranen Saudiyyah ba amma wannan shine karo na farko da harin tayi sanadiyar mutuwar wani.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng