Magidanci ya matsa layar zana bayan matar sa ta haifi 'ya'ya uku rigis
Wani magidanci, Paul Edobor; mai shekaru 44, ya gudu ya bar matar sa, Ugoma, bauan ta haifi 'ya'ya uku rigis.
Kafin haihuwar 'ya'ya ukun, Ugoma; 'yar asalin jihar Abiya, sun haifi 'ya'ya biyu tare da mijinta Paul, cikin shekaru goma da yin aurensu.
Ugoma ta isa ofishin kungiyar 'yan jarida dake Benin a jihar Edo, dauke da 'ya'ya ukun, duk mata, tare da neman taimako a wurin jama'a.
"Mijina ya ki ya dawo gida sannan ya ki daukan kira na. Ya gudu ne saboda ba zai iya daukan dawainiyar 'ya'yan ba. Tun bayan haihuwa ta yaki ya dawo ko ya dauki kirana," inji Ugoma.
DUBA WANNAN: Bikin aure uku da suka girgiza Najeriya a watan nan
Ta kara da cewar, tun bayar gudun mijin nata jama'a ne ke tallafa mata wajen kulawa da jariran.
"Ina yawo coci da kasuwa da yaran domin neman taimako. Ina rokon mijina ya dawo duk inda yake. Ni na yafe masa duk abinda ya faru. Mun riga munyi aure kuma mutu ka raba," a cewar Ugoma.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng