A Karo Na Biyu, Bill Gates Ya Sake Yiwa Gwamnatin Nigeria Kaca-Kaca

A Karo Na Biyu, Bill Gates Ya Sake Yiwa Gwamnatin Nigeria Kaca-Kaca

Mutum na biyu da ya fi kowa kudi a duniya, wato Bill Gates, ya sake caccakar gwamnatin tarayyar Nigeria kan gazawarta a bangaran ilimi da kiwon lafiya.

A wata hira da gidan jaridar CNN ta yi da shi jiya talata, Bill Gates yace: "Tsarin farfado tare da bunkasa tattalin arziki na gwamnatin Nigeria, na daya daga cikin muhimman abubuwan dake janyo saka hannun jari daga mutanen mu. Amma ayyukan da gwamnati ta baiwa fifici, ba su da alaka da inganta bukatun yan kasa. Gwamnati ta baiwa ayyuka na zahiri fifiki sama da wanda zai inganta rayuwar al'umma.

A Karo Na Biyu, Bill Gates Ya Sake Yiwa Gwamnatin Nigeria Kaca-Kaca
Bill Gates da Buhari

Bill Gates ya cigaba da cewa "mutanen da ba su da tituna, tashar jirgin ruwa da masana'antu, ba yadda za su iya cigaba. Amma fa tituna da tashoshin jiragen ruwa da masana'antu, ba za'a iya gina su da gudanar da su ba sai da ma'aikata masu cikakkiyar lafiya, fikira da ilimi. Da su ne kadai tattalin arziki zai dore"

Sai dai kuma cikin hirar da ya yi da CNN, hamshakin mai kudin ya bayyana cewa duk da haka, tattalin arzikin Nigeria kan iya cigaba da bunkasa idan gwamnati ta baiwa bangaren lafiya da ilimi fifiko.

DUBA WANNAN: Gwamna Dankwambo ya dauki nauyin jinyar almajirin da aka datsewa hannaye

"A dan alakar da nayi da najeriya, na fahimci tsarin tattalin arzikinta bashi da inganci sosai. Nigeria na da zakakuran matasa masu jini a jika. Amma daga inganci har dan adadin da ake tsakurowa don cigaban matasa da bangaren lafiya da ilimi bai taka kara ya karya ba. In suka iya samun kiwon lafiya da ilimi yadda ya dace, za su fi kowa a Africa"

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng