Jami'an NSCDC sun damke wasu matsafa biyu a jihar Kwara

Jami'an NSCDC sun damke wasu matsafa biyu a jihar Kwara

Jami'an hukumar tsaro na NSCDC reshen jihar Kwara ta gano wani gidan matsafa a garin Aleyo da ke Layin Ojoko a karamar hukumar Asa na jihar ta Kwara bayan wani mutum da aka damfara N5m a gidan tsafin ya kai kuka wajen hukuma.

Kwamandan hukuma ta NSCDC, Mr. Ayinla Adeyinka wanda yayi magana ta bakin kakakin hukumar, Mr. Ayodele Bello ya shaidawa mananema labarai a ilorin cewa jami'an hukumar sun kai samame gidan ne bayan wani Mr. Muminu Abdulrahman ya shigar musu da kara.

An gano wasu matsafa biyu a jihar Kwara
An gano wasu matsafa biyu a jihar Kwara

A cewar kwamandan, jami'an NSCDC sun gano dakunan safi tare abubuwan tsafi masu ban tsaro da tayar da hankali.

KU KARANTA: An damke dan Najeriya da miyagun kwayoyi na N800,000 a kasar Indiya

Ya kuma ce an kama mutane biyu a gidan tsafin, Mr. Kazeem Abdulsalam mai shekaru 54 mazaunin Omu-Aran a karamar hukumar Irepodun da kuma Mr. Adamu Hussein mazaunin Marafa Ojo a karamar hukuma Ilorin ta gabas.

Kwamandan ya yi ikirarin cewa Abdulsalam ya amsa laifin tsafi da kuma damfarar al'umma kudaden su da sunnan zai rubanya musu kudaden.

Adeyinka ya kara da cewa hukumar ta NSCDC tare da gwamnatin jihar za tayi duk mai yiwuwa don ganin an binciko musababin abin da ake aikatawa a wurin, ya kuma yi gargagadi da al'umma su guji fadawa hannun yan damfara da matsafa wanda za suyi alkwarin azirta su.

Sai dai kuma shi Abdulsalam ya shaida wa manema labarai cewa ba gidan tsafi bane, ya ce suna taimaka su al'umma masu matsalan aljanu ne kuma suna bayar da wurin haya ga masu yin fina-finai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164