Gwamna Dankwambo ya dauki nauyin jinyar almajirin da aka datsewa hannaye

Gwamna Dankwambo ya dauki nauyin jinyar almajirin da aka datsewa hannaye

Gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, y ace zai biya dukkan kudaden da za a kashe yayin jinyar wani almajiri mai shekaru 12 da aka datsewa hannaye bayan ya samu rauni daga horon da malamin makarantar su ya yi masa.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewar Dankwambo ya dauki wannan alkawari ne yayin day a kai ziyarar dubiya ga almajirin, Zubairu Abubakar, a asibitin koyarwa na na FTH, jiya, litinin, a garin Gombe.

Almajiri Zubairu ya rasa hannayensa bayan samun mummunan lahani daga daurin da malaminsa, Sirajo Muhammad, ya yi masa bisa zargin ya saci waya.

Gwamna Dankwambo ya dauki nauyin jinyar almajirin da aka datsewa hannaye
Gwamna Dankwambo

Sanadin daurin ne ya saka Zubairu kamuwa da kwayoyin cuta da suka shiga jikinsa ta hanyar raunin day a samu, dalilin day a saka likitoci a asibitin koyarwa na FTH bayar da shawarar yanke hannayensa kacokan.

DUBA WANNAN: Aure uku da suka girgiza Najeriya a watan nan

Gwamna Dankwambo, da kwamishinan shari’a a jihar, abdulhameed Ibrahim, ya wakilta, y ace ya ziyarci asibitin ne domin ganin halin da yaron yake ciki tare da bayyana cewar gwamnatin jihar Gombe zata shiga maganar domin daukan dukkan matakan shari’a da suka dace.

Ya bukaci iyayen yaron das u yi hakuri tare da basu tabbacin cewar gwamnatin jihar zata yi iyakar kokarinta wajen taimakon yaron.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng