Gwani na gwanaye: An samu ɗalibai masu shaidar digiri mai daraja ta daya daga jami’ar Bayero

Gwani na gwanaye: An samu ɗalibai masu shaidar digiri mai daraja ta daya daga jami’ar Bayero

Jamiar Bayero ta gwamnatin tarayya dake jihar Kano ta yaye gwanayen dalibai, hazikai kuma zakakurai guda 72 da suka samu shaidar digiri mai daraja ta daya, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Shugaban jami’ar, Farfesa Yahuza Bello ne ya bayyana haka a yayin wata ganawa da manema labaru, a ranar Litinin 26 ga watan Maris, a shirye shiryen gudanar da bikin yaye dalibai 8,635, karo na 34.

KU KARANTA: Magidanci ya aikata ma kansa saɓalikta, ya ɗirka ma ɗiyarsa ciki, ya bindige ɗansa Magidanci ya aikata ma kansa saɓalikta, ya ɗirka ma ɗiyarsa ciki, ya bindige ɗansa

Farfesan ya bayyana cewar za’a gudanar da bikin ne a ranakun 3 zuwa 7 ga watan Afrilun bana, daga cikin daliban da za’a yaye, 5,401 sune masu digiri na farko, sai masu digiri na biyu su 1,833, da kuma masu digirin digirgir su 70.

Gwani na gwanaye: An samu ɗalibai masu shaidar digiri mai daraja ta daya daga jami’ar Bayero
Bikin yaye daliban jami’ar Bayero

Sai dai Farfesa Yahuza Bello yace hukumar gudanarwar jami’ar ta yanke shawarar ba zata bayar da digirin girmamawa ba ga manyan mutane kamar yadda aka saba a baya ba, ba wai don babu wadanda suka cancanta ba, amma saboda su kara martaba digirin da jami’ar ke bayarwa.

Bugu da kari Yahuza ya bayyana cewar a karkashin jagorancinsa, jami’ar ta samu gagarumar nasarori ta bangaren cigaba, inda ta samu sahhalewar hukumar kula da jami’o’in Najeriya (NUC) game da wasu kwasakwasai 15 na digiri, da kuma 8 na gaba da digiri.

Daga karshe shugaban jami’ar ya kara da cewa a shekarar 2918, jami’ar Bayero ta dauki dalibai guda 8,600, wanda hakan kari ne ga adadin daliban da suke dauka a baya, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng