Soji sun musanta zargin da akeyi musu na taimakawa Makiyaya a Taraba
- Mutanen jihar Taraba sun zargi jami’an Soji da tallafawa Makiyaya dake kisan mutane a jihar
- Mazauna jihar sun kuma zargi Sojin dake atisayen Ayem A’Kpatuma (Tseren kyanwa) da cin mutuncin mutane
- Sojin sun musanta wannan zargin da mutanen wannan jihar ke masu
A ranar Litinin 27 ga watan Maris, wasu daga cikin mazauna jihar Taraba, sun zargi jami’an Ayem A’Kpatuma (Tseren Kyanwa) ma’aikatan Soji na jihar suna cin mutuncin mutane, kuma suna bawa Makiyaya kwarin gwiwa wurin kaiwa mutane hari.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Ciyaman din kungiyar Takum na jihar Taraba, Shiban Tikari, yace kiran Janar Danjuma ya tsorata jama’ar Takum.
KU KARANTA: Ku kare kan ku daga masu kokarin kashe ku: TY Danduma ya fadawa 'yan Najeriya
“Kafin gudanar da aikin, akwai korafe korafe na maganar satar mutane, fashi da makami, wanda akeyi ta hanyar amfani da kayan ‘Yan Sanda da kuma na Soji. Hakan ya sanya mutane dayawa idan Sojin sun tsayar dasu sais u dauka cewa ‘yan fashi ne ko barayi kuma hakan ya kawo matsaloli da far gaba a tsakanin mutane.
“Ina da rahotanni akan Soji sun shiga gidajen mutane cikin dare, suna ci masu mutunci, amma kuma sai gashi a gaban barikin Soji aka sace dan majalisar jiha, Hossa Ibi aka kasheshi”, inji Tikari.
Wani kuma mazaunin, Rimamsikwe Karma, Ciyaman na kungiyar Ussa, yace aikin da ake gudanarwa yana cutar da mutane fiye da taimaka masu.
Jagoran kungiyar Sojin na bataliya ta 93, Takum, Lt. Col Ibrahim Gambari, yace bashida da hurumin yin magana akan lamarin, amma kuma ya karyata zargin da akeyi masu.
Legit.ng ta ruwaito cewa, Ciyamomin Takum da Wukari, Shiban Tikari da Daniel Adi, a ranar Lahadi, 28 ga watan Janairu, sun tsallake rijiya da baya a jihar Taraba, inda ‘yan bindiga suka kusa halakasu a wurare daban daban na jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng