Kotu ta daure wanda ke sojan gona da sunan sarkin kano na tsawon watanni 36
- Kotu a jihar Kano ta daure wani matashi mai aikata sojan gona da sunan sarkin kano har na tsawon watanni 36
- Kotun ta sameshi da aikata laifuka uku, Sojan Gona, Yaudara, da kuma Canja Kama
- Wanda ake zargin ya amsa laifinsa a gaban kotu, ya roki sassaucin hukunci daga kotun, inda aka yanke masa daurin shekara daya ko kuma tarar N30,000
Kotu a jihar Kano, ranar Litinin ta yankewa wani dalibi, Sultan Bello, mai shekaru 20, hukuncin dauri na tsawon watanni 36, bisaga Sojan Gona da yakeyi da sunan sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II.
Kamfanin dillancin lbaran Najeriya (NAN), ta bada rahoton cewa, wanda ake zargin mazaunin Ja’oji New Court Road Quarters ne, a jihar Kano, wanda kotun ta sameshi da aikata laifuka guda uku, Sojan Gona, Yaura, da kuma Canja Kama.
Wanda ake zargin ya amsa laifukansa a gaban kotun, ya kuma sassaucin hukunci daga kotun, inda kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekara daya ko kuma tarar N30,000, bisaga laifin Canja kama.

Alkalin ya kuma bukaci wanda mai laifin daya shirya da mutane shidan dake kararsa akan yanda zaya biyasu kudadensu da ya karba N1.85m.
Mai gabatar da kara, Haziel Ledapwa, ya fadawa Kotu cewa wanda ake zaigin ya aikata laifin ne a ranar 27 ga watan Fabrairu.
Yace,mai laifin ya aikata shi ne ta hanyar yin amfani da kafar sadarwa ta Instagram, inda ya ringa nuna kansa a matsayin sarkin Kano.
KU KARANTA KUMA: Karfin hali barawo da sallama: Kotu ta yanke ma dalibin da yayi ma Sarkin Kano sojar gona
“Bello ya nemi N1.4m da hannun Barka Sani, N150,000, daga Sadiq Saflan, N50,000, daga Sadiq Sani, 50,000, daga Aisha Ahmad, N50,000, daga Surajo Zakari, N150,000, daga Yahaya, sune aka hada suka bayar da N1.85m”.
Ledapwa yace, wanda ake zargin ya karba kudaden ne da sunan wata mai was an finafinai ta hausa, Zubaida Mu’azu, wadda ya nuna ta masa waka ne a matsayinsa na sarkin kano. Ya kuma bukaci mutanen da su biya kudaden ta asusun ajiyarta na First Bank, mai lamba 3049986447. Mai gabatar da kara yace laifin ya sabawa sashe na 132, 322 da kuma 392 na dokar kasa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng