Mavrodi, Mutumin da ya gudu da biliyoyin Nairorin 'yan Najeriya ta hanyar MMM, ya mutu

Mavrodi, Mutumin da ya gudu da biliyoyin Nairorin 'yan Najeriya ta hanyar MMM, ya mutu

Dan kasuwar kasar Rasha, Sergei Mavrodi, da ya kirkiri tsarin MMM da ya talauta mutane da dama a kasar Rasha da Najeriya, ya mutu.

Mavrodi ya fara kirkirar tsarin MMM a shekarun 1990 kuma tun a wadancan shekarun ya damfari mutanen kasar Rasha kudi masu yawa ta hanyar tsarin.

Rahotanni sun bayyana cewar an garzaya da Mavrodi asibiti bayan ya yi korafi da ciwo a kirjinsa, sannan ya mutu bayan wasu wasu sa'o'i, kamar yadda kafar watsa labarai a kasar Rasha suka sanar.

Mavrodi, Mutumin da ya gudu da biliyoyin Nairorin 'yan Najeriya ta hanyar MMM, ya mutu
Sergei Mavrodi

An zabi Mavrodi a matsayin dan majalisa a shekarar 1994. Ya rasa kujerar sa a shekarar 1996.

A shekarar 2007, wata kotu a birnin Moscow ta tabbatar da Mavrodi a matsayin dan cuwa-cuwa tare da yi masa hukunci.

DUBA WANNAN: An kori dan sandan da ya bindige wani yaron mota daga aiki

A shekarar 2011, Mavrodi, ya kara bude tsarin MMM da ya kaddamar a kasashen India, China, Afrika ta kudu, Zimbabwe, da kuma Najeriya.

A duk kasashen, Mavrodi, ya rufe tsarin bayan jama'a sun narka kudi masu yawa cikin tsarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: