Mallakar bindiga a kasar Amurka ya zama tamkar ruwan dare
- Dunbin masu zanga-zanga na cigaba da yin tururuwa a ciki da wajen biranen kasar Amurka
- Zanga-zangar da suka saka mata suna "Mu yi tattaki don kare rayukan mu"
- Matakin mallakar bindiga a kasar ta Amurka domin kare kai ya haddasa cece-ku-ce a kasar, inda da yawa suke ganin a hana mallakar bindigar ma gaba daya, sai dai kuma wasu a kasar suna ganin haramta mallakar bindigar kamar wani yunkuri na tauye hakkin dan adam
Dunbin masu zanga-zanga na cigaba da yin tururuwa a ciki da wajen biranen kasar Amurka, don tilasta gwamnatin kasar ta kara tsaurara dokar da take baiwa 'yan kasar damar mallakar bindiga cikin sauki.
DUBA WANNAN: Sojojin Saudiyya sun samu nasarar dakatar harin makamai masu linzami guda 7 na 'yan tawayen Houthi
Zanga-zangar da suka saka mata suna "Mu yi tattaki don kare rayukan mu", na zuwa ne bayan da wasu dalibai su 17 suka rasa rayukan su a Parkland dake jihar Florida ta kasar Amurka, hakan ya biyo bayan harin da wani dan bindiga ya kai makarantarsu.
Ma zauna kasar sun shirya gabatar da zanga - zangar a bisa rukunin kungiyoyi sama da 800 a ciki da wajen kasar ta Amurka, inda a yanzu haka taron zanga - zangar ya yi karfi a biranen London, Tokyo, Geneva, Edinburgh da kuma birnin Sydney.
Matakin mallakar bindiga a kasar ta Amurka domin kare kai ya haddasa cece-ku-ce a kasar, inda da yawa suke ganin a hana mallakar bindigar ma gaba daya, sai dai kuma wasu a kasar suna ganin haramta mallakar bindigar kamar wani yunkuri na tauye hakkin dan adam.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng