Gwamnan Sokoto da PDP ke zawarci ba zai bar Jam’iyyar APC ba
- Da alama cewa Gwamna Tambuwal bai zai nemi kujerar Shugaban kasa ba
- Mai magana da yawun bakin Gwamnan ya maidawa Sahara Reporters martani
- Hadimin Gwamnan ya nuna cewa Mai gidan sa ba zai yi takara da Buhari ba
Mun samu labari cewa Gwamnan Jihar Sokoto da Jam'iyyar PDP mai adawa ta ke zawarci ya nuna ba zai bar Jam'iyyar sa ta APC mai mulki. Mun fahimci cewa Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Kasar ba zai sauya sheka ba zuwa Jam'iyyar adawa.
Gwannan na Jam'iyyar APC da ake sa rai zai yi takarar Shugaban kasa a zaben 2019 da Shugaba Muhammadu Buhari ya ba tsohuwar Jam'iyyar sa ta PDP kunya bayan da mai magana da yawun bakin sa Imam Imam ya musanya rade-radin da ke yawo.
KU KARANTA: Yele Sowore zai fito takarar Shugaban kasa a 2019
Kwanaki Jaridar Sahara Reporters ta rahoto cewa Jam'iyyar PDP ta kammala shirin dauko Tambuwal a matsayin 'Dan takarar ta a zaben Shugaban kasa mai zuwa. Imam Imam ko da ra'ayin sa yake fada ya nuna cewa Tambuwal ba zai yi takara a PDP ba.
Malam Imam Imam ya bayyanawa Jaridar Sahara Reporters wanda mai-gidan Jaridar watau Yele Sowore ke shirin fitowa takarar Shugaban kasa cewa ya shirya gwabzawa ne da Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019 ba Gwamnan na Jihar Sokoto ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng