Mutane 6 sun mutu yayin kokarin gina dakin amarya a Sokoto
A kalla mutane shida ne suka mutu a garin Illela-Kalmalo dake karamar hukumar Illela a jihar Sokoto.
Mutanen sun mutu ne bayan da gabar kasa ta zaftaro, ta fado a kansu yayin da suke hakar kasa domin gina dakin amaryar abokinsu dake shirin angoncewa.
Wani shaida, Malam Hamza Illela, ya sanar da manema labarai cewar mutum daya ya tsira ba tare da samun rauni ba.
Wadanda tsautsayin ya ritsa da su sun hada da; Bashar Buhari, Isah Amadu, Abdullahi Salihu, Bashar Dalhatu, Bashar Maciji, da Bilyaminu Jadi.
Tuni aka binne su bisa tsarin addinin Islama.
"Al'adar mu ce a yi taron gayya domin taya mutum yin gini a auren shi na farko. Muna yin hakan a matsayin taimako da kuma agaji ga shi angon.
"Suna cikin hakar kasar nan sai kawai ta zaftaro ta danne su, tsautsayi ne da kuma karar kwana, kuma tuni an binne su kamar yadda addini ya tanada," a cewar wani mazaunin kauyen da bai yarda a ambaci sunansa ba.
DUBA WANNAN: Ana sace kaso 50% na man fetur da muke turowa Aba-Enugu ta bututu - NNPC
Shugaban karamar hukumar Illela, Alhaji Abdullahi Haruna Illela, ya tabbatar da faruwar al'amarin tare da shaidawa majiyar mu cewar yana daga cikin mutanen da suka halarci jana'izar mutanen har ma ya bayar da gudunmawa ga iyalansu.
Daga bisani ya yi addu'ar Allah ya ji kansu, ya yafe kura-kuransu, ya kuma bawa iyalinsu hakurin jure rashin su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng