Tsarin tattalin arzikin Shugaba Buhari bai ba kiwon lafiya da ilmi muhimmanci ba – Bill Gates

Tsarin tattalin arzikin Shugaba Buhari bai ba kiwon lafiya da ilmi muhimmanci ba – Bill Gates

Mun samu cikakken jawabin da Attajirin Duniya Bill Gates yayi a Daily Trust a kan Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wanda yace an yi sakaci da ilmi da kiwon lafiya. Kalaman na sa dai sun jawo abin magana yanzu haka a kasar.

Bill Gates ya fara ne da yabawa yadda Najeriya ta bunkasa a fannin fasaha. Attajirin yace ‘Yan Najeriya na da burin cewa kasar za ta gyaru sai dai wannan bai isa ya sa kasar ta canza a dare guda ba sai Gwamnatin Tarayya tayi namijin himma.

Tsarin tattalin arzikin Shugaba Buhari bai ba kiwon lafiya da ilmi muhimmanci ba – Bill Gates
Kalaman Bill Gates sun jawo surutu a Najeriya

Mai kudin Duniyar ya nemi Gwamnatin Shugaba Buhari ya dage wajen habaka harkar ilmi da lafiya domin jama’a su zama mutane. Bill Gates yace Najeriya na cikin inda su ka fi ko ina wahala wajen haihuwa saboda rashin kula da kiwon lafiya.

KU KARANTA: An rasa inda Shugaban bangaren Jam’iyyar APC a Kaduna ya shige

Attajirin ya kara da cewa a Najeriya kashi 1 cikin 3 na ‘Yan Najeriya na fama da yunwa ban da kuma larurar rashin lafiya. Dalilin haka ne Bill Gates yace idan Gwamnati ba tayi wani yunkuri ba Najeriya za ta samu kan ta cikin matsala nan gaba.

Hamshakin mai kudin na Duniya ya bayyana cewa tsarin tattalin arzikin Gwamnatin Buhari ba zai ko ina ba don kuwa ba ayi la’akari da inganta harkar lafiya da ilmi ba. Gates ya nemi a dauki kwararrun Malaman lafiya kuma a biya su albashi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng